Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tashi daga Abuja zuwa N’Djamena

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tashi daga babban birnin tarayya Abuja zuwa N’Djamena babban birnin kasar Chadi don jagorantar babban taron shugabanin kasashen yankin tafkin Chadi.

Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin sa na jagora a babban zauren taron, shi ne ya bada umarnin da gaggauta yin taron a yau don samar da hanyoyin da za’a dakile ayyukan kungiyar Boko Haram, bayan da ya halacci taron manyan hafsoshin tsaron kasar nan a jihar Borno.

Mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan kafafen yada labarai Mr Femi Adesina ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar aAbuja cewa za’a gudanar da taron shugabanin kasashen yakin tafkin Chadi a  yau Alhamis don shawo kan matsalar tsaro da ya addabi yankin.

Haka kuma sanarwar ta bayyana cewar shugaban kasar Benin zai halacci taron kasancewar kasar na bada gudunmawar sojoji wajen yaki da ‘yan ta’adda.

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO