Dalibi ya kashe kansa yayin da yake shekarar karshe a jami’a

Hukumar gudanarwar jami’ar UNIBEN da ke jihar Edo ta tabbatar da mutuwar daya daga cikin daliban ta wanda ake zarkin ya kashe kansa ne a cikin daki.

An dai gano gawar dalibin ne mai suna Adams a cikin dakin sa da ke yankin Ekosodin a karamar hukumar Ovia ta arewa maso yamma a jihar ta Edo.

Haka kuma rahotannin sun bayyana cewa dalibin na shekarar ta biyar ne a jami’ar inda ya ke karantar ilimin nazarin kwamfuta.

Wasu shaidun gani da ido sun shaidawa manema labarai cewa an yiwa Adams ganin karshe ne lokacin da ya mika aikin da aka bashi ga malamin sa kana ya koma wurin kwanan dalibai inda daga nan ke kuma ba’a kara jin duriyar sa ba.

Sai dai daga bisani aka gano gawarsa bayan da ‘yan uwansa suka ziyarce shi bayan da suka balla kofar dakin da ya ke ciki.

Sai dai a lokacin da hukumar makarantar ke tabbatar da faruwar al’amarin ita kuwa rundunar ‘yan sandan jihar bata ce komai ba kan mutuwar dalibin.

The short URL of the present article is: http://freedomradionig.com/default/frpjcsk

Opinion Polls

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO