Gwamnatin tarayya ta dauki gabaran tattaunawa da kungiyar Bokon haram

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin sa ta dauki gabaran tattaunawa da kungiyar Boko-Haram domin ceto ‘yan matan Sakandaren Dapchi wadanda aka sace su a makarantar su a kwanakin baya.

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya bayar jiya a Abuja.

 

A cewar sanarwar, shugaba Buhari ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke maraba ga sakataren harkokin wajen Amurka Mr. Rex Tillerson a fadar shugaban kasa ta Asorok da ke Abuja.

 

Sanarwar ta kuma ruwaito cewa tuni gwamnatin tarayya ta tuntubi kungiyoyin kasa da kasa da masu shiga tsakani domin tattaunawa kan hanyoyin da za a bi wajen sakin ‘yan matan.

 

Shugaba Buhari ta cikin sanarwar dai ya kara da cewa a cikin makwannan zai kai ziyara makarantar da lamarin ya faru domin jajantawa iyayen yaran.

The short URL of the present article is: http://freedomradionig.com/default/frlIDgR

Opinion Polls

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO