Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Jam’iyyar PDP ta goyi bayan karramar da shuga Buhari yayi wa MK Abiola

Published

on

Jam’iyyar adawa ta PDP ta ce dari bisa dari ta goyi bayan duk wata karrama wa da za a yiwa wanda ake zaton ya lashe zaben shugabancin kasar nan da akayi na ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1993 wato MKO Abiola.

 

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar Mista Kola Olgbondiyan ya fitar a jiya Lahadi.

 

Sai dai jam’iyyar ta ce tayi alla wadai da matakin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya duka na yi amfani da bada lambar Yabon domin cimma muradun sa na siyasa a shekarar 2019.

 

Inda ta ce bayar da wanna lambar yabo wadda ya kamata a ce tun a baya aka bada ita kamar dawo da hannun agogo baya ne kuma ba zai karawa shugaban kasar wani karsashin a harkar siyasa ba.

 

Haka kuma a lokacin da jam’iyyar ta PDP ke taya iyalan Abiola murnar karrama shi da aka yi da sauran wadanda suka yi shahadar siyasa lokacin zaben 12 ga wan Yunin, jam’iyyar ta bukaci da a tuna mutane irin su Sanata Abrahma Adesanya, da Bagauda Khalto, da kuma Dan Sulaiman sai Raph Obirah Alex Iburu da sauransu.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!