Majalisar wakilai ta janye dakatarwar da ta yiwa Abdulmumin Jibrin kofa

Majalisar wakilai ta janye dakatarwar da ta yiwa dan majalisa mai wakiltar Kiru da Bebeji daga jihar Kano Abdulmumin Jibrin.

Wannan na zuwa ne biyo bayan wasikar ban hakurin da dan majalisar Abdulmumin Jibrin ya aikewa majalisar.

Duk da cewa shugaban majlisar be karanta dukkanin abinda wasikar ta kunsa ba yayin zaman majalisar, sai dai yace ya bawa majalisar hakuri, kuma ya gabatar da duk wasu matakai da majalisar ta bukace shi ya bayar.

A cewar shugaban majalisar Yakubu Dogara bayan ya gama karanta wasikar, majalisar ta bashi damar cigaba da zuwa bakin aikin sa a duk lokacin da yake bukata.

A shekarar 2017 ne majalisar wakilan ta dakatar da dan majalisar Abdulmumin Jibrin halartar duk wani zama da zatayi, sakamakon bayyana zargin da yayiwa majalisar na cewa tayi cushe cikin kunshin kasafin kudi.

The short URL of the present article is: http://freedomradionig.com/default/frJPkHt

Opinion Polls

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO