Menu Close

Shugaba Buhari ya ja kunnen yan siyasa kan yakin neman zabe

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga yan siyasa a kasar nan da kada su sanya Najeriya cikin rudani da tashin hankali yayin yakin neman zabe da hukumar INEC ta bada umarni farawa daga jiya Lahadi.

A cewar shugaban Kasar shekaru hudun da za a sake yi a sabuwar gwamnati na da mutukar muhimmaci ga al’ummar kasar nan.

Shugaban kasar na wadannan kalamai ne yayin da yake kaddamar da fara yakin neman zabensa a karo na biyu  a fadar  Aso Rock da ke birnin tarayya Abuja.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce zabin da al’ummar kasar nan za su yi a shekara mai zuwa zai taimaka wajen dai-daita al’amuran tsaron da tattalin arziki a kasar nan.

Shugaban kasar ya ce shawarar da zai baiwa dukkanin yan takarar a kasar nan da kada su duba banbacin jam’iyya, su kuma sanya muradun kasa a gaba wajen yakin neman zaben su.