Menu Close

Yan takarar shugaban kasar Najeriya za su tafka muhawara ranar 19 Janairun badi

Kungiyar shirya muhawara kan siyasa ta kasa ta ware ranar 19 ga watan Janairun shekarar 2019 a matsayin ranar da ‘yan takarar shugabancin kasar nan da suka tsaya karkashin inuwar jam’iyyu daban-daban za su gudanar da mahawara.

Haka zalika kungiyar ta kuma ware ranar 14 ga watan Disambar bana a matsayin ranar da mataimakan ‘yan takarar shugabancin kasa kuma za su gudanar da ta su muhawarar.

Shugaban kungiyar Mr. John Momoh ne ya bayyana hakan, lokacin da yake jawabi yayin wani taron manema labarai yau Alhamis a birnin tarayya Abuja.

Mr. Momoh wanda shi ne shugaban kungiyar kafafen yada labarai na rediyo da talibijin na Najeriya, ya ce, taron muhawarar za a gudanar da shi ne a dakin taro na Transcorp da ke Abuja, kuma za a nuna shi tare da sanya muryoyin su kai tsaye a gidajen talibiji da rediyo da ke karkashin shugabancin kungiyar a fadin Najeriya.

Ana sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sake tsayawa takarar shugaban kasa karkashin inuwar jami’iyyar APC da Atiku Abubakar na babbar jam’iyyar adawa ta PDP za su halarci taron muhawarar.