Menu Close

INEC:ta kori mai tattara sakamakon zaben karamar hukumar Bokkos dake jihar Filato

Hukumar zaben mai zaman kanta ta kasa INEC ta kori Farfesa Musa Izam a matsayin mai tattara sakamakon zabe a karamar hukumar Bokkos dake jihar filato 

Rahotanni sin yi nuni da cewa Izam wanda malamin komiyya ne a jami’ar Jos ya yi yunkurin gujewa sanar da sakamakon zaben karamar hukumar, sai dai matasan da ke yankin suka iza keyarsa zuwa cikin hukumar suka hanashi guduwa.

A cewar jami’in hukumar ta INEC a jihar ta Filato Mista Osaretin Imahiyerobo, ya zama wajibi su kori farfesan sakamakon buguwa da yayi a dalilin shaye-shaye da ya hana shi ci gaba da gudanar da aikin nasa.

Ya kuma ce hukumar ta INEC za ta dauki matakin gaggawa domin ganin ba a saamu matsala wajen tattara sakamakon zaben a yankin ba.

 Ya kuma ce suna jaran farfesan ya dawo garin Jos ya kuma yi musu bayanin dalilan dasuka sanyashi ya yi wannan danyen aiki kafin daukar mataki na gaba.