Menu Close

Kotun daukaka kara: Sanata Ademola ya cancanci tsayawa takara a zaben da ya gabata

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta ce dan takarar gwamnan jihar Osun karkashin jam’iyyar PDP Sanata Ademola Adeleke ya cancanci tsayawa takara a yayin zaben gwamnan da aka gudanar a jihar a shekarar da ta gabata.

Kotun mai kunshe da alkalai uku ta amince da daukaka karar da Sanata Ademola Adeleke da kuma jam’iyyar sa ta PDP su ka yi.

Da ya ke karanta sakamakon hukuncin mai shari’a Emmanuel Agim ya kuma ce kotun ta bukaci wadanda suka shigar da kara gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja wato wahab Raheem da Adam habib da su biya Sanata Adeleke tarar naira miliyan 3.