Menu Close

Fasinjoji 19 sun mutu sanadiyyar hatsatin mota a jihar Ondo

Akalla mutane 19 ne suka rasa rayukansu sakamakon wani hatsarin mota da ya ritsa da su akan titin Akure zuwa Owo a jihar Ondo.

Rahotanni sun ce mutanen sun kone kurmus yadda ba za a iya gane su ba sanadiyar hadarin da ya faru a jiya Asabar.

Mai magana da yawun hukumar kiyaye abkuwar hadurra ta kasa reshen jihar Ondo, Mr. Femi Joseph, ya ce, tuni aka kai gawawwakin mutanen zuwa babban Asibitin jihar Ondo da ke garin Akure.

A cewar sa, hatsarin ya shafi wata motar safa kirar Toyota mai dauke da fasinjoji goma sha takwas, wanda ke kan hanyar zuwa Abuja da kuma wata motar dakon kaya.

Mai magana da yawun rundunar kiyaye abkuwar hadurra ta kasa reshen jihar ta Ondon, ya kuma ce, motocin biyu sun yi taho mugama ne wanda a sanadiyar haka motar safa din ta kama da wuta wanda kuma dukkannin fasinjojin da ke cikinta suka kone kurmus.