Menu Close

An soki Jami’an tsaro da Hukumar zabe kan zaben Jihar kano EU

Kungiyar tarayyar Turai EU ta soki jami’an tsaro da Hukumar zabe ta Najeriya INEC game da rawar da suka taka yayin zaben gwamnan karo na biyu da aka gudanar a nan jihar Kano.

A yayin gabatar da rahoto kan zabuka Najeriya da suka gudana a farkon wannan shekara, kungiyar ta EU ta ce, kodayake Najeriya an samu ci gaba wajen gudanar da zabuka  fiye da zabukan da suka gabata, amma akwai wasu bangarori da ya kamata Hukumar ta gudanar da gyare-gyare a zabuka na gaba.

A cewar kungiyar ta EU jami’an tsaro sun gaza wajen kare lafiya da dukiyar jama’a yayin zaben gwamnan karo na biyu da aka yi a jihar Kano.

Kungiyar tarayyar Turai ta kuma ce Hukumar zabe ta kasa INEC da jami’an tsaro sun kyale jam’iyyun siyasa da ‘yan daba sun ci karar su ba babbaka wajen tada hatsaniya a lokacin zabe.

A wani labarin kuma, fadar shugaban kasa ta ce, shugaba Muhammadu Buhari ya gamsu da sakamakon rahoton kungiyar tarayyar Turai akan manyan zabukan kasa da suka gudana a wannan shekara.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai Magana da yawun babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu.

Sanarwar ta ce shugaba Buhari, ya sha alwashin cewa zai yi duk me yiwuwa don ganin an gudanar da sauye-sauye da za su kara inganta ayyukan Hukumar zabe ta kasa INEC.

Sai dai anata bangaren jam’iyyar PDP ta ce har yanzu tana kan bakatar cewa an tabka magudi yayin manyan zabukan kasa da suka gudana.