Menu Close

Borno:kimanin mutane 30 ne suka mutu a wani hari da aka kai yankin Konduga

Wasu hare-haren Bam wanda ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka kai su, sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 30 a yankin Konduga da ke jihar Borno.

Shugaban sashen gudanar da ayyuka na hukumar bada agajin gaggawa na jihar Usman Kacalla ne ya bayyana hakan a yau Litinin, inda ya ce a Yanzu haka yawan wadanda suka rasa ransu sakamakon harin ya kai 30.

Ya kuma kara da cewa kimanin mutane 40 ne kuma suka jikatta wanda ya karu akan mutane 17 da aka samu tun da fari.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan kunar bakin waken sun fasa bam din da ke jikin su a wajen wani gidan Kallo da ke yankin Konduga na yankin kudu maso gabashin jihar ta Borno lokacin da mutane ke tsaka da kallon bal.