Menu Close

Kotu ta ware ranar 5 ga Yuli a matsayin ranar yanke hukuncin karar gwamnan Jihar Osun

Kotun koli ta ware ranar biyar ga watan gobe na Yuli a matsayin ranar da zata yanke hukunci kan karar da dan takardar gwamnan jihar Osun na jam’iyyar PDP wato Ademola Adeleke ya daukaka gaban ta.

Mista Adeleke ya shigar da kara gaban kotun kolin ne yana mai kalubalantar hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a ranar tara ga watan Mayun da ya gabata, na tabbatar da Adegboyega Oyetola a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar gwamnan jihar ta Osun.

Kotun mai alkalai bakwai, karkashin jagorancin mukaddashin babban jojin Najeriya mai shari’a Ibrahim Muhammad ta ware ranar da zata yanke hukunci kan karar, bayan da alkalan suka gudanar da muhawara kan hakan.

Idan za’a iya tunawa dai a baya kotun daukaka kara tayi watsi da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke da ta ayyana Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar ta Osun, bayan da Hukumar INEC ta ayyana gwamnan mai ci Adegboyega Oyetola  a matsayin wanda ya lashe zaben.

Kamar yadda rahotanni suka nuna ayau litinin ne aka tsammaci hukuncin kotun kan shari’ar da Mista Adeleke ya daukaka zuwa gaban ta, biyo bayan kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara da yayi.