Menu Close

Hukumar LRCN ta kalubalanci jami’o’i kan su mayar da dakunan karatu na zamani

Hukumar rijistar dakunan karatu ta kasa LRCN, ta kalubalanci jami’o’in Najeriya da su mayar da hankali wajen  mayar da dakunan karatu na zamani ta hanyar amfani da kwamfuta domin bunkasawa tare da ciyar da harkokin kimiyya gaba.

Shugaban hukumar ta LRCN, Farfesa Michael Afolabi ne ya bayyana hakan a yau, yayin bikin bude taron horarwa na kwanaki 4 da aka shirya ga ma’aikatan mai take Amfani da na’urorin zamani wajen adana bayanai.

Farfesa Michael Afolabi ya ce, amfani da fasahar zamani wajen adana bayanai abu ne da ba zai misaltu ba, don haka ne hukumar ta shirya horarwar domin koyar da ma’aikatan yadda za su rika amfani da fasahar sadarwar a wuraren ayyukan su.

Da yake jawabi yayin taron, shugaban jami’ar Bayero ta Kano Farfesa Muhammad Yahuza Bello wanda mataimakinsa na bangaren gudanarwa Farfesa Haruna Wakili ya wakilta yace taron ya zo ne a kan gaba duba da irin muhimmancin da yake da shi ta fuskar bunkasa ilimi.

Wasu daga cikin wadanda suka halarci horarwar sun bayyana cewa, za su koyar da abokan aikin su da basu samu haron ba wasu daga cilin abubuwan da suka koya tare da yin amfani da su a wuraren ayyukan nasu.

Taron wanda aka gudanar a jami’ar Bayero da ke nan Kano, ya samu halartar ma’aikatan jami’o’in kasar nan da daga jami’o’i daban-daban.