Menu Close

Gwamnatin tarayya ta bayyana kudaden da ake kashewa wajan shigo da madara

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa adadin kudaden da ake kashewa duk shekarar wajen shigo da madara da dangogin ta daga ketare ya tasamma Dala Biliyan daya da miliyan dubu dari uku.

Babban sakatare a ma’aikatar noma da raya karkara ta tarayya Dakta Mohammed Umar ne ya bayyana hakan, lokacin da yake jawabi yayin babban taron hada-hadar madara a nahiyar Afirka karo na hudu, wanda ya gudana a birnin tarayya Abuja.

Taron mai taken bunkasa hanyoyi zuba jari wajen yin hada-hadar madarar a nahiyar Afirka, ya mayar da hankali kan yadda za’a bullo da wasu sabbin matakai da zasu taimaka wajen bunkasa kasuwancin madarar da dangogin ta a duniya ba wai nahiyar Afirka kadai ba.

Babban sakataren ma’aikatar noman Dakta Muhammad, wanda ya samu wakilcin daraktan sashen lura da al’amuran kiwon dabbobi Mista Bright Wategire ya bayyana cewa an bullo da matakan shirya taron ne da nufin tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan yadda za’a inganta kasuwancin madara da dangogin ta.

A cewar sa kasuwancin madarar na fuskantar kalubale da dama, don haka akwai bukatar mayar da hankali sosai a bangaren noma da kiwon dabbobi, kasancewar hakan zai taimaka wajen inganta bangaren.