Menu Close

Ofishin jakadancin Najeriya da ke kasar Jamus ya bukaci bayanai kan harin da aka kaiwa Ike Ekweremadu

Ofishin jakadancin Najeriya da ke kasar Jamus ya bukaci hukumomi a kasar Jamus din, da su fito da bayanan wadanda aka kama da hannu wajen cin zarafin sanata Ike Ekweremadu a kasar ta jamus ranar 17 ga watan Agustan da muke ciki.

A wata sanarwa da ofishin jakandancin kasar nan ya fitar a birnin Berlin,ta ce ofishin ya kuma bukaci a hukunta masu laifin dai-dai da dokokin kasar ta Jamus.

Haka kuma Ofishin ya kuma bukaci hukumomin kasar ta jamus da su tsananta bincike don gano hakikanin masu laifin don hukunta su yadda ya dace.

Ofishin jakadancin Najeriya a kasar Jamus ya kuma ce gudanar da bincike da hukunta masu laifin zai karya gwiwar masu yunkurin yin irin hakan a nan gaba.