Menu Close

Buhari ya nada Abdulrahman Baffa Yola a matsayin mai takaimakasa a harkokin siyasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nada Abdulrahaman Baffa Yola a matsayin mai taimaka masa na mussaman kan al’amuran siyasa

 

Wannan na kunshe cikin wasaikar da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya sanya wa hannu mai dauke da sha tara ga wannan wata da muke ciki na Agusta.

 

Kunshin wasikar ta bukaci wanda aka nada Abdulrahaman Baffa Yola da rubanya kokarin sa wajen sauke nauyin da aka dora masa wajen bunkasa siyasar kasar nan.

 

Haka zalika wasikar ta ce nadin nasa zai fara aiki ne nan take kuma zai kare da zarar gwamnati mai ci wa’adin ta ya kawo karshe.

 

A cikin wasikar sakataren gwamnatin tarayya ya taya Abdulrahaman Baffa Yola murnar samun wannan cigaban.

 

Kafin nadin nasa Abdurahamn Baffa Yola na rike da mukamin maitaimakawa na mussaman kan al’amuran gwamnati a ofishin mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo.