Menu Close

Gwamnan Nasarawa ya kira taron gaggawa kan harin da aka kaiwa mataimakinsa

Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya kira taron gaggawa kan harin da aka kai wa mataimakin sa Dr, Emmanuel Akabe wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 5.

 

Wannan na kunshe ne cikin sanarwar da sakataren yada labaran sa Yakubu Lamai cewa gwamnan ya kira taron gagawa ne don sake karafafa tsaro a jihar.

 

A yayin taron sa safiyar yau Laraba gwamnan ya baiwa al’ummar jihar tabbacin tsaro da lafiyar ‘yan jihar ta Nasarawa.

 

Rahotanni sun bayyana cewar a dai kwanakin baya ne majalisar dokoki ta jihar ta yi kira ga gwamnan jihar ta sake rubanya kokari kan matsalar tsaro na jihar kasancewar masu satar mutane da yin garkuwa da su, sun yi yawa a jihar ta Nasarawa.