Menu Close

wasu yan fashi sun kai hari ga kwanbar motocin mataimakin gwamnan Nasarawa

Wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne sun kai hari ga kwanbar motocin mataimakin gwamnan jihar Nasarawa Dr, Emmanuel Akabe yayin da suka kashe jami’an ‘yan sanda 3.

 

Mataimakin gwamnan wanda yake kan hanyar sa ta zuwa Abuja don yin wani aiki yayin da ‘yan fashin suka kai musu harin kilimita kadan zuwa Akwanga da misali karfe 6 na yammacin jiya Talata.

 

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Nasarawa ASP Usman Sama’ila ya tabbatar da afkuwar al’amarin ga manema labarai a garin Lafiya.

 

Sai dai ASP Usman Sam’ila bai bada cikakken rahoto kan faruwar al’amrin ba, amma ya ce kwamshinan ‘yan sanda jihar Bola Longe ya jagoranci jami’an ‘yan sanda don tantance yawan asarar da aka yi a wurin.