Labaran Kano
Sarki Muhammadu Sunusi II ya amsa takardar tuhumar da gwamnatin Kano ke masa
Mai martaba sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi ll ya musanta zargin da Hukumar karbar korafi da yaki da cin hanci da rahsawa ta jihar Kano ke masa na barnatar da sama da naira biliyan uku mallakin masarautar Kano.
Wannan na kunshe cikin takardar tuhumar da sarkin ya amsawa gwamnatin jihar Kano, mai dauke da sa hannun mukaddashin sakataren majalisar masarautar Kano Malam Abba Yusuf.
A cewar sarkin lokacin da ya hau karagar mulkin Kano, ya samu naira biliyan daya da miliyan dari takwas da casa’in da uku, da dubu dari uku da talatin da takwas, da dari tara da ashirin da bakwai, da kuma kwabo talatin da takwas a lalitar masarautar.
Mai martaba sarkin Kano ta cikin takardar ya kuma bayyana cewa shi ba jami’in lura da sashen kudi bane, don haka bashi da alhakin yadda za’a sarrafa kudin masarautar Kano.
Idan za a iya tunawa dai a ranar Alhamis din da ta gabata ne gwamnatin jihar Kano ta aikewa Malam Muhammadu Sanusi na biyu takardar tuhumar, kan zargin da ake masa da barnatar da sama da naira biliyan uku mallakin masarautar, tun daga lokacin da ya hau mulki zuwa yanzu.
Labaran Kano
An bukaci a daga darajar kwalejin ilimi ta Nasiru Kabara zuwa jami’a

Dan majalisar dattijai mai wakiltar yankin Kano ta Kudu Sanata Barau Jibrin ya bukaci shugaban darikar kadiriyya ta Afrika Sheikh Kariballah Sheikh Nasir Kabara da ya daga darajar kwalejin ilimi ta addinin musulunci da ya fara ginawa zuwa jami’a.
Dan majalisa Barau Jibrin ya bayyana hakan ne a wajen bikin Maukibi da mabiya darikar Kadiryya suke gudanarwa duk shekara da aka gudanar a yau.
Sanata Barau Jibrin ya ce abin alfahari ne yadda aka fara samun mutane irin su Sheikh Kariballah da suke da kishin ilimin addinin musulunci suna irin wannan yunkuri na bunkasa addinin musulunci, a don haka ne shima yayi alkawarin rubanya aikin ginin har sau uku matukar aka daga darajar kwalejin zuwa jami’a.
Barau Jibrin ya kuma ce matasa na matukar bukatar irin wadannan jami’o’I na addinin musulunci don kaifafa kwakwalwar su, kan ilimin addinin musulunci da kuma harkokin kimiyya da fasaha
Sanata mai wakiltar kudancin Kano ya kuma nuna takaicin sa kan yadda ake da jami’o’in addinin musulunci biyar kachal a Najeriya a lokaci guda kuma ake da na addinin kirista guda 34, yana mai cewa akwai bukatar al’ummar musulmi su dage wajen gina jami’o’in addinin musulunci.
Labaran Kano
Sulhu tsakanin al’umma zai rage cunkoso a kotuna

Wata kungiya mai rajin ganin an tabbatar da gaskiya da adalci dake garin Kumbotso, ta ce samar da kungiyoyin al’umma da zasu dinga aikin sulhunta jama’a zai taimaka wajen rage yawan yadda ake shigar da kararraki gaban jami’an tsaro da ma masu unguwanni a jihar Kano.
Shugaban kungiyar Isyaku Ahmad ne ya bayyana hakan ta bakin sakataran kungiyar dake kula da tsare-tsare Iliyasu Nuhu, yayin taron jin ra’ayin jama’ar garin na Kumbotso kan ayyukan da kungiyar ta sanya a gaba.
Ilyasu Nuhu ya ce a yanzu ana yawan samun shigar da kararraki gaban jamian tsaro kan dan abinda za’a a iya magance shi ta hanyar sulhu, amma sai batun ya yi zafin da har sai anje gaban kotu, yana mai cewa hakan na taka rawa wajen samar da cunkoso a gaban kotuna.
Wasu daga cikin mahalartar taron sun bayyana cewa wannan sabon tsarin zai taka rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kuma fahimtar juna tsakanin al’ummar yankin.
Wakilin mu Abubakar Tijjani Rabi’u ya ruwaito cewa taron ya samu halartar shugabannin addinai daban-daban da kungyoyin kare hakkin dan adam dana yaki da cin hanci da rashawa da sauran al’umma.
Labaran Kano
Ku kasance masu yin kasuwanci kamar yadda addinin musulunci ya koyar

An shawarci ‘yan kasuwa da sauran ma’aikata da su kasance masu gudanar da harkokin kasuwancinsu irin yadda addinin musulunci ya koyar domin kaucewa fadawa cikin fushin ubangiji a ranar gobe kiyama.
Shugaban cibiyar koyar da zaman Aure da kasuwanci a addinin Musulunci Dakta Yahya Tanko ne ya bayyana hakan yau lokacin taron bita tare da wayar da kan ‘yan kasuwa da ma’aikata kan tarbiyyar addinin musulunci a cikin harkokin kasuwanci.
Ya kara da cewa abin takaici ne yadda ‘yan kasuwa a yanzu suke gudanar da harkokin kasuwancin su, wanda hakan ya sauka daga layin koyarwa irin ta addinin musulunci.
A cewar Dakta Yahya Tanko kamata ya yi duk wani musulmi a ko ina yake ya zama tamkar mudubi da kowacce al’umma zata rika koyi da shi ta fuskar kasuwanci.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito cewa malamai da ‘yan kasuwa da ma’aikata da dama ne suke halarci taron.
-
KannyWood2 months ago
An fara sulhu tsakanin jaruman da suka yi auren mutu’a
-
KannyWood2 months ago
Abinda yasa ‘yansanda suka cafke Sadiya Haruna
-
KannyWood2 months ago
Abinda ya sanya ba zan iya auren Yawale a zahiri ba -Rayya
-
KannyWood2 months ago
Yadda akayi auren mutu’a a Kannywood
-
Labarai2 months ago
An garkame Sadiya Haruna a gidan yari
-
KannyWood2 months ago
Kun san abinda ya hana jaruma Maryam Yahya aure?
-
Manyan Labarai2 months ago
An gano wanda ya fito a bidiyon da ake zargin Daurawa ne
-
Labaran Kano1 month ago
Kotu ta yankewa matashi hukuncin kisa a Kano