Connect with us

Kasuwanci

Bankin Unity ya baiwa abokan huldarsa hakuri bisa gobarar da ta tashi a shalkwatarsa

Published

on

Da safiyar yau Litinin ne gobarar ta tashi a shelkwatar bankin na Unity da ke jihar Lagos kamar yadda rahotonni suka bayyana .

Sanarwar bada hakurin na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin bankin na twitter.

Sanarwar ta ce, bankin na baiwa al’umma hakuri bisa wannan iftila’i da ya fada ma sa, kuma yana iya kokarin wajen ganin komai ya daidaita.

Tuni dai hukumar kashe gobara ta jihar ta Lagos ta kai daukin gaggawa don kashe wutar, tare da bayyana cewa babu asarar rai sakamakon tashin wutar.

Continue Reading

Kasuwanci

An fara kera Fensir a Najeriya

Published

on

Wani kamfani a nan  gida Najeriya ya fara kera fensira ta hanyar amfani da tsaffin jaridu .

 

Ministan kimiyya da fasaha Dr. Ogbonnaya Onu ne ya bayyawa cewar kamfanin zai fara samar da akalla pensira fiye da miliyan biyu a duk shekara wanda ya fi karfin amfani birane da yankuna kadai.

 

Da yake Magana jiya a Abuja yayin da ya karbi bakuncin gangun wani kamfanin da ke samar da pensira na Bamib ya ce’ mun yaba da yadda kake gudanar da ayyukanka na cigaban kasa.

 

Ya ce a wata ziyara da suka kai wani kamfanin samar da fensira a jiha Enugu , ‘mun tarar da su suna gudanar da bincike akan fensira, abin takaici ne sakamakon kasar nan bata da wani kamfani da ke samar da fensira a Najeriya .

 

A da akwai wasu kamfanunuwa da suke sarrafa fensira amma dukkaninsu sun dakushe a yanzu, hakan ce ta sa a matsayina na ministan kimiyya da fasaha na ga dacewar sarrafa shi a Najeriya duba da yadda daliban mu na firamare da ma wasu yan sakandare da ke amfani da fensir.

 

Minister Onu ya ce a ganinsa fensir ba wani a zo a gani ba, ya kuma zama wajibi a ce Najeriya tana samar da fensiran da take amfani da su.

 

Ya ce mun basu shekara biyu domin samar da adadin fensiran da ake bukata, yana mai cewa samar da fensiran ya dauki hankali na, domin kuwa duk kayayyakin da ake kera fensiran muna da shi a Najeriya, hakan dai zai samar da ayyukan yi ga matasa

 

Ministan ya ce kawo yanzu an samu cigaba domin zasu tabbatar da cewar an samar da dukkanin kayayyakin a nan gida Najeriya, tare da cewar tuni gwamnatin Akwa Ibom suka fara kira fensira wanda wannan wani cigaba ne.

Continue Reading

Kasuwanci

Kamfanin TCN ta tallata gwanjon jirage masu saukar ungulu

Published

on

Jirgi mai saukar ungulu

Bayan shafe shekaru na halin ko in kula da kamfanin samar da  wutar lantarki ta kasa ,wanda ta gada daga tsohowar kamfanin wutar lantarki NEPA na wasu  jirage masu saukar ungulu guda hudu, wanda kudadensu ya kai kimanin dala dubu dari bakwai da ashiri kwatankwacen fiye da Naira miliyan dari biyu da hamsin da biyu, wanada za’a yi gwanjon  su.

 

Jiragen mallakin hukumar samar da wutar lantarki ta  sun bayyana kudirinsu na gwanjon wadannan jirage mai kirar BO-105 , da suke ajeye a filin jiragen saman na cikin gida dake Murtala Muhammad a jihar Lagos.

 

Jaridar Punch ta rawaito cewar jiragen saman masu saukar ungulu da ake amfani da su wajen kai kawon duba kayyakin wutar lantarki tare da aiwatar da wasu gyare-gyare a fadin kasar nan , suna nan zaune ne ba tare da ana amfani da su ba na tsawon lokaci.

 

Biyu daga cikin jiragen masu dauke da lamba 5N-ASK da 5N-ASJ rabon da suyi yi aiki tun a shekara ta 1995-1997, kuma an kira su ne a  shekara 1978.

Kamfanin TCN ya ce wasu kwantenoninsa guda biyu sun yi batan dabo

Kamar yadda hukumar samar da wutar lantarkin  ta ce, babu fa’ida na a gyara su, mai makon haka, kamata yayi a sayar da su a akan kudi dala dubu dari a halin da suke ciki.

 

Ragowar jiragen kuwa guda biyu masu lambar ta rijista 5N-BCj da 5N-EPA suna ajeye ne tun shekara ta 2008 kuma za’a iya sayar da su a kan kudade dala dubu dari uku da arbain da kuma dala dubu dari da tamanin.

 

Su kuma an kira su ne a shekara ta 1996 da kuma 1993 suma gyara wanda za’a iya gyara su domin suyi aiki amma na dan lokaci.

 

Hukumar dai a ‘yan kwanakin nan ne suka fitar da gayyatar masu saye domin su zo su saye.

 

A dai kwanakin baya ne  tawagar gwamnati daga  bangaren sharia suka je suka duba jiragen masu saukar ungulu a ranar Asabar din da ta gabata domin duba su kafin a fara gwanajan su.

 

Haka zalika Shugaban  kwamitin majalisar datijjai dake kula da wutar lantarki sanata Yusuf Yusuf dake wakiltar Taraba ta tsakiya ya ce makasudin ziyarar shi ne  domin duba lafiyar jiragen  kafin a sayar da su.

 

Ya kara da cewa daga cikin abinda suka gani za’a yi iya gwanjon biyu daga cikin su , amma ragowar kuwa za’a iya sayar da su a matsayin ‘yan gwangwan

Continue Reading

Kasuwanci

Zaben shugaba Buhari ne yasa kungiyar IPOB ta rika cin mutuncin yan kasuwar Arewa.

Published

on

 

Hadaddiyar kungiyar yan kasuwar arewacin Najeriya tace zuwan shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya saka suka kafa hadaddiyar kungiyar yan kasuwar  domin magance matsalolin da ke fuskantar arewacin Najeriya da yan kasuwar su.

Mataimakin shugaban kungiyar yan kasuwa na arewacin Najeriya Jahi Abdullahi ne ya bayyana haka lokacin da yake tattaunawa da filin Barka da Hantsi na Freedom Radio.

Malam Jahi Abdullahi ya kara da cewa dalilin da yasa ake cin mutuncin nasu shugaba Buhari bayan an rantsar da shi a watan Mayun shekarar 2015.

Yace lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi mulki an rika yi musu zargin da babu gaira babu dalili daga ciki har da ambatar su da sunan yan Boko haram da cin mutunci iri iri.

Jahi Abdullahi ya kara da cewa dalilin da yasa kenan suka kafa kungiyar haddaddiyar yan kasuwa ta arewacin na Najeriya inda yace a yanzu lamarin ya riga ya kau.

A sakamakon haka sai da ta kai sun ga Gwamnan jahar Abia Ikpeazu Ikeazu wanda bai ji dadin irin cin zarafin da kungiyar tabbatar da yan kasar Biafra ta IPOB ta rika yi musu ba.

Sun  kuma koka da yadda baa baiwa al’ummar arewacin Najeriya damar gudanar da kasuwanci a yanayi mai kyau a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

A nasa bangaren shugaban kungiyar ta jahar Kano Isah Haruna yace zasu cigaba da jajircewa domin taimakawa yan kasuwar jahar Kano da arewa gaba daya.

Continue Reading

Now Streaming

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.