Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Kananan yara miliyan 821 ne basa samun isashshan abinci-kungiyar dalibai

Published

on

Kimanin  yara miliyan 821 ne basa samun isasshen abinci a Duniya sakamakon rashin wayewar bayar da abinci da ya kamata.

Shugaban kungiyar dalibai masu karantar lafiyar abinci na jami’ar Bayero ta Kano Auwalu Musa Umar, ne ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da filin  Barka da Hantsi na Freedom Radio a safiyar Litinin 23 ga watan Satumba.

Auwalu Musa Umar ya ce daga cikin abubuwan da mata masu dauke da juna biyu ke mantawa shi ne irin abincin da ya kamata su ci lokacin da suke dauke da juna biyu.

Auwalu Musa Umar ya kara da cewa idan har mata bayan haihuwa za su rika shayar da yara yadda ya kamata to za a  magance mutuwar jarirai miliyan 52 a Duniya.

Sannan kungiyar daliban masu karantar harkokin lafiyar abinci ta kuma gargadi mata da kada su bar yara kanana suna kwanciya da yunwa wanda hakan yake tasgaro ga lafiyar su.

 

Rahoto :Abbas Yushau Yusuf

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!