Connect with us

Kiwon Lafiya

Meke hadassa Tabin hankali ?

Published

on

Binciken da hukumar lafiya ta duniya ta yi ya, ya nuna cewar Najeriya na daya daga cikin kasashen da ake fama da masu tabon hankali a duniya, bayan da masu fama da cutar suka kai fiye da miliyan daya.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewar ana samun karuwa da masu dauke da wannan cutar musamman ma a kasashen Afrika ta yamma ciki har da nan gida Najeriya.

Haka zalika binciken ya sake bayyana cewar likitoci dari biyu ne ke duba  kusan mutane miliyan dari biyu dake kamuwa da wannan cutar.

Wakiliyar mu Aisha Muhammad ‘Yanlema ta ttauna da kwararran likitan kwakwalawa na Asibitin koyar na Aminu Shehu Ibrahim Kano Dr, Aminu Ibrahim yayin da ake bikin ranar masu tabon hanakali ta duniya.

Kiwon Lafiya

An yiwa daya daga yaran Kano da aka sace fyade

Published

on

Daya daga cikin yara tara da aka ceto a garin Onitsa dake jihar Anambra, ta fuskanci cin zarafi na fyade a hannun wanda suka sace ta, kamar yadda cibiyar da ke lura da wadanda suka fuskanci matsala ta fyade ta bayyana.

 

Manajan cibiyar Nasiru Garko ne ya bayyanawa jaridar Kano Focus cewar, bayan duba daya daga cikin yaran yar shekara 10 domin tabbatar da ba ta dauke da wasu cutuka da ake samu ta hanyar cin zarafi.

 

Ya ce yarinya ta bayyana cewar an aikata fyade da ita sau da dama daga hannun wanda ya sace ta.

Malam Garko wanda likita ne ya tabbatar da faruwar hakan.

Yaran da aka sace sun kaiwa Ganduje ziyara

 

An dai kafa wannan cibiyar ne a karkashin kulawar asibitin kwararru na Murtala Muhammad dake nan Kano.

 

Kawun yarinyar wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce babban burinsu shine a bi musu hakkinsu dangane da garkuwa da akayi da yarsu.

 

Ya na mai cewa zasu tattaua don ganin an shigar da kara akan cin zarafi da aikata fyade da aka yi akan ‘yar ta su.

 

 

 

Continue Reading

Kiwon Lafiya

Abubuwan da ya kamata ku sani gami da lafiyar Idanu

Published

on

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ware kowa ce ranar alhamis ta mako na biyu a watan Oktoba a matsayin ranar gani ta duniya da nufin wayar dakan al’umma kan matsalar gani da yadda ya kamata su kare kansu daga cutuka da ka iya jawo cutar makanta.

Kazalika ranar tana maida hankali ne kan yadda za a taimakawa masu lalurar gani acikin al’umma.

Continue Reading

Kiwon Lafiya

Mutane 36 ne suka kamu da zazzabin ciwon shawara a Katsina

Published

on

Mutane 36 ne suka kamu da zazzabin ciwon shawara a Katsina

Akalla mutane 36 ne suka kamu da zazzabin ciwon shawara a wasu kananan hukumomin guda biyu na Danmusa da Kankara da ke jihar katsina

Mataimakin gwamna jihar Katsina Mannir Yakubu ne ya bayyana haka a yayin da ya ke kaddamar da aikin riga kafin zazzabin ciwon shawara a makon da ya gabata.

Mataimakin gwamna ya ce kaddamar da riga kafin wani yunkuri ne da gwamnatin su ta dauka domin dakile yaduwar cutar zazzabin ciwon shawara.

Ya ce ana kyautata zaton aikin riga kafin zai kai ga akalla mutane miliyan bakwai, inda yake jaddada cewar zazzabin ciwon shawara zazzabi ne mai yaduwa wanda ake daukarsa ta hanyar cizon wasu nau’ikan sauro da ke cizon mutane.

Mataimakin gwamna wanda babban sakataren ma’aikatar lafiya ya wakilce shi Dr Kabir Mustapha, ya bukaci al’umma da su tabbatar da sun kare kansu da kamuwa da wannan ciwo ta hanyar karbar riga kafin zazzabin ciwon shawara , wanda yake kyauta ne, ake kuma bukatar ‘yan shekaru 9 zuwa 44 ne zasu karbi wannan riga kafin.

Da yake gudanar da jawabinsa a yayin kaddamar da wannan riga kafin, shugaba harkar sadarwa na asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya Musa Rabiu ya tabbatar da bada ta su gudumuwar wajen aiki da gwamnatin jihar ta Katsina don wayar da kan al’umma dangane da matsaloli kiwon lafiya da ke addabar yan jihar.

Continue Reading

Now Streaming

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.