Connect with us

KannyWood

An gano Jakadiyan Tona Asiri

Published

on

An gano Jakadiyan Tona Asiri

Cikin wani sautin muryar tattaunawar waya ta juramin fina-finan Hausa Isa A. Isa ya bayyana cewa jarumar nan da ta yi fice a shafukan sada zumunta wato Sadiya Haruna ta san wanene Jakadiyyan Tona Asiri kuma suna da alaka da ita.

Saurari tattaunawar ta Isa.

Jakadiyyan Tona Asiri dai wani asusu (account) ne da ya jima a dandalin sada zumunta na Instagram wanda yake wallafa bayanan Gulma da Tsegumi musamman a masana’antar Kannywood, al’umma da dama dai na son ganin shin ko wacece ko waye wannan Jakadiya?

Tunda farko dai wani rikici ne ya barke a tsakanin Isan da kuma Sadiyar inda kowa ke kokarin tona asirin dan uwansa.

Ita ma a nata bangaren cikin wani sakon murya da ta aikewa Jakadiyar Tona Asiri, Sadiyar ta yi maganganu da suke gab da gasgata maganar Isan.

Saurari jawabin Sadiya.

Izuwa yanzu dai tuni wannan batu ya fara daukar hazo a shafukan sada zumunta inda jama’a suke ta bayyana ra’ayoyi mabam-bamta akai.

Allah ya kyauta.

Rubutu mai alaka:

An fara sulhu tsakanin jaruman da suka yi auren mutu’a

An gano wanda ya fito a bidiyon da ake zargin Daurawa ne

Kun san abinda ya hana jaruma Maryam Yahya aure?

Continue Reading

KannyWood

Ina fatan Allah ya bani sana’ar da tafi Kannywood -Mansur Makeup

Published

on

Fitaccen jaruminnan Bello Muhammad Bello wanda aka fi sani da BMB dan jihar Filato ya nuna takaicinsa kan yadda ya ce ba’a baiwa jaruman masana’antar Kannywood kulawa ba, a yayin taron gangamin yaki da cutar Cancer da aka gabatar a birnin tarayya Abuja karkashin jagorancin uwar gidan gwamnan jihar Kebbi Hajiya Zainab Bagudu.

Wannan batu na General BMB ya janyo cecekuce musamman a shafin sa na Instagram inda fitaccen mai kwalliyar nan Mansur MakeUp yazo yayi tsokaci kamar haka.

“Wannan gaskiyane General amma kaima ka san da laifin mutanenmu don suna gani akayi haka kuma baza su yi magana ba kamar yadda kace saboda kar don abinda za’a basu a hanasu kokuma don kada akara kiransu kwadayi yayi mana yawa talauci ya yawaita a Kannywood ALLAH kabamu sana’ar da tafi ta samu da kuma albarka”

Rubutu masu alaka:

Da gaske Adam Zango ya dauki nauyin karatun dalibai?

Kun san abinda ya hana jaruma Maryam Yahya aure?

Abinda ya sanya ba zan iya auren Yawale a zahiri ba -Rayya

Continue Reading

KannyWood

Da gaske Adam Zango ya dauki nauyin karatun dalibai?

Published

on

Mahukunta a makarantar Farfesa Ango Abdullahi dake Zaria, sun tabbatar da cewa jarumin fina-finan Hausa Adam A. Zango ya dauki nauyin karatun dalibai marayu guda 101 a makarantar.

Yayin tattaunawar da Freedom Radio tayi da shugaban makarantar Mallam Hamza Jibril ya tabbatar mana da cewa sun samu takarda daga dauke da bayanan cewa Adam Zango yana son zai dauki nauyin karatun dalibai har guda 101, kuma bayan da suka gama tattaunawa tuni Adam Zangon ya biya kudin tun a makon da ya gabata.

Dangane da daliban da za’a dauki nauyin karatun nas Mallam Hamza ya bayyana cewa Adam Zango ya baiwa masarautar Zazzau gurbin mutane 50 sai jam’iyyar APC aka bata gurbin mutane 31 sai kuma jam’iyyar PDP da aka baiwa mutane 20.

Dukkan su bisa sharadin zasu kawo dalibai marayu, ko talakawa da iyayen su basu da ikon biya musu kudin makaranta.

Haka zalika Mallam Hamza ya karyata dukkan rahotonnin dake yawo a soshiyal midiya na cewa batun daukar nauyin karya ne ba gaskiya bane.

Duk kokarin da Freedom Radio tayi na jin ta bakin jarumin Adam A. Zango amma abin ya ci tura, sai dai wani makusancinsa ya tabbatar mana da cewa Adamun ya dauki nauyin wadannan dalibai.

Tun a yammacin jiya ne dai labaran yake ta yawo a sohiyal midiya na cewa a damun ya dauki nauyin karatun daliban inda wasu ke ta gasgata labarin wasu kuma ke karyatawa.

Takardun shaidar biyan kudin da Adam Zango yayi.

RUBUTU MAI ALAKA:

Na taba yin soyayya da Maryam Yahaya a baya –Mai Shadda

Abinda ya sanya ba zan iya auren Yawale a zahiri ba -Rayya

Kun san abinda ya hana jaruma Maryam Yahya aure?

Kun san dalilan da suka sanya aka garkame Sadiya Haruna a gidan yari?

Continue Reading

KannyWood

Muhimman abubuwan da suka faru a Kannywood cikin makon da ya gabata

Published

on

A ranar Asabar ne aka rintsar da sabbin shuwagabannin ƙungiyar masu shirya finafinan Kannywood ta Nijeriya, wato MOPPAN, biyo bayan zaben da aka gudanar a garin Dutse babban birnin jihar Jigawa.

Tsohon shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa (NFVCB) shiyyar arewa-maso-yammacin ƙasar nan, Dakta Ahmad Sarari, shi ne ya lashe zaɓen zama shugaban kungiyar ta MOPPAN inda yayi nasarar kan abokin takararsa kuma shugaban ƙungiyar da ya nemi yin ta-zarce, wato Alh. Abdullahi Maikano Usman, Wanda tuni ya aike da sakon taya murna ga sabon shugaban.

Dakta Sarari dai yayi alkawarin sake bunkasa kasuwar fina-finan Hausa da kuma kara fadada tasirin masana’antar zuwa sauran jihohi, sannan yayi alkawarin ganin ya magance dukkan matsalolin dake addabar masana’antar ta Kannywood.

Dakta Ahmad Sarari Sabon Shugaban Kungiyar Moppon

(more…)

Continue Reading

Now Streaming

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.