Connect with us

Labarai

Labarin Zakunan da  suka taba ballewa a fadar shugaba Buhari.

Published

on

A satin da muka yi bankwana da shi ne zaki ya balle daga kejinsa a gidan ajiye namun daji na   jahar Kano, kafafan yada labarai da dama ne suka bayar da Labaran ballewar zakin daga gidan namun dajin na jahar Kano.

Rahotanni sun yi nuni da cewa wannan zaki ya koma ma’ajiyarsa da kansa duk da gayyato masu allurar kashe jiki ta manyan dabbobi irin su zaki da kwararru suka yi daga Abuja, da sauran gurare da aka yi gayyar.

Zakin na gidan adana namun dajin ya tayar da hankalin al’umma daban daban har su kansu al’ummar yankin basu samu kwanciyar hankali ba, sakamakon sanarwar cewa su kula da abunda kaje ya kawo kafin a kame zakin da garkame shi.

Manyan namun daji irin su zaki da zakanya na bukatar kula yadda ya kamata ,shin gidan namun daji na jahar Kano , wacce matsala da ya kamata a shawo kanta tun fil azal an yi nasara.

A zamanin mulkin Janar Abdussalami Abubakar rikakkun zakuna sun taba ballewa daga kejin da suke inda suka rika ruri a harabar fadar ta shugaban kasa ,har ta kai tsohon shugaban kasa janar Abdulsalami Abubakar hankalin sa ya kai ga zakunan da bayar da umarnin harbe su.

Malam Yahaya Zariya na daya daga cikin maaikatan fadar shugaban kasar Najeriya a lokacin da zakuna suka ballle a fadar.

A binciken tarihi da Freedom radio tayi ya nuna cewa Malam Yahaya na aiki a fadar shugaban kasa tun lokacin birnin tarayya na Legas, a fadar Dodan Barrack.

Lokacin da shugaban kasa Janar Ibrahim Babangida ya dawo da mazaunar Gwamnatin tarayya a Abuja malam Yahaya mutumin Zariya ya cigaba da aiki a lambun fadar Shugaban Najeriya.

Malam Yahaya yace a lokacin mulkin marigayi Janar Sani Abacha an bashi kyautar jariran zakuna daga kasar Sierra leone zamanin mulkin Ahmad Tijjani Kabbah.

Sannan marigayi Shugaba Abacha ya siyo wasu jariran zakuna da Malam Yahaya ya cigaba da kula da su har suka rika.

A bibiyar Tarihin da gidan rediyan Freedom yayi tace lokacin da zakunan na fadar Shugaban Najeriyar suka rika kuma Malam Yahaya na kiwon su sai da masana ilimin dabbobin daji suka umarce shi da ya rage kusantar wadannan namun daji sakamakon rika da suka yi.

Mai kula da zakunan yace sakamakon sabawa da yayi da Zakunan na fadar shugaban kasa, bai daina kusantar suba domin shi yake ciyar da su abinci a wannan lokaci ta hanyar yanka musu raguna.

Malam Yahaya mai aiki a fadar ta shugaban kasa ya kara da cewa wata rana an samu kuskure a fadar ta shugaban Najeriya zamanin mulkin janar Abdulsalami Abubakar ,sai Zakunan suka balle aka kasa shawo kansu a fadar ta shugaban kasa.

Hakan ya jawo hankalin tsohon shugaban kasa Janar Abdulsalami Abubakar inda ya bayar da umarnin rundunar sojan dake tsaran fadar ta shugaban kasa da su harbe Zakunan na fadar ta shugaban kasar.

Jin haka hankalin Malam Yahaya mutumin Zariya ya tashi saboda kaunar da yake yiwa wadannan zakuna.

Malam Yahaya ya yi ta maza, ya sai da rai, inda ya shiga kejin Zakunan na fadar shugaban kasa ya yi wa Zakunan kiranye sai suka biyo shi suka shiga ,shi kuma yayi sauri ya rufe kofar ya fuce ta wata.

 

Labarai

Shugaba Buhari ya jajantawa alummar Garkida

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa al’ummar kauyen Garkida na jihar Adamawa da kungiyar Boko Haram ta kaiwa hari.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai Garba Shehu ya fitar jiya a birnin tarayya Abuja.

Ta cikin sanarwar, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce shakka babu sojojin kasar nan sun mai da hankali kan rage wa mayakan Boko Haram karfi a yankunan arewa maso gabashin kasar nan.

Shugaba Buhari ya ce ya zama wajibi a yabawa jami’an tsaron kasar nan kan yadda suke aiki ba dare ba rana wajen tabbatar da zaman lafiya.

Yaki da cin hanci da rashawa bana Buhari ba ne- Ministan Ruwa

Buhari Bai Damu Da Harkokin Lafiya Ba-Likitocin Yara

Shugaba Buhari ya gana da sufeton yan sanda ta kasa kan arangamar yan Shi’a

Muhammadu Buhari ya kara da cewa, nan da wani dan lokaci Gwamnati zata kaddamar da kamfe kan yakar ta’addanci.

Shugaban kasa ya kuma yi kira ga al’ummar kasar nan wajen ci gaba da baiwa jami’an tsaro goyon baya na kare dukiya da tsaron lafiyar ‘yan kasar nan.

Continue Reading

Labarai

Kai tsaye: Cigaba da bikin yaye daliban jami’ar tarayya ta Dutse

Published

on

Note: Ana cigaba da sabinta wannan shafi, ku cigaba da bibiya


Dalibai guda dari 786 ne jami’ar tarayya ta Dutsen jihar Jigawa, ke bikin yayewa a yau.

Rahotanin sun bayyana cewar, daga cikin dalibai dari bakwai da tamanin da shida (786) da ake bikin yayewa, hamsin da biyu (52) sun samu digiri mai matakin daraja ta farko wato First Class.

Kuma wannan shi ne karo na 5 da jami’ar ke bikin yaye dalibai.

Yanzu haka ana dab da kammala wannan biki da dake gudana a babban dakin taro na jami’ar.

A jawabin da ta gabatar, na yau Asabar shugabar jami’ar, Farfesa Fatima Batulu Muktar ta bayyana farin cikinta, tare da godiyar ta ga mahalarta taron inda ta bayyana irin nasarori da jami’ar ta samu musamman a bangaren ilimi da sauran bangarori na ci gaban jami’ar.

Farfesa Batulu Mukhtar ta kuma mika godiyar ta ga abokan hulda musamman gwamnatin jihar Jigawa da sauran dai-daikun al’umma da suka bada gudunmuwa wajen ci gaban jamiar.

Ku kalli hotuna daga wurin taron na yau:

Continue Reading

Labarai

Mata basu fiya karbar rashawa ba -Muhuyi Magaji Rimin Gado

Published

on

Gwamnatin jihar kano ta yi kira ga al’umma a ko wane mataki da su tashi tsaye domin yaki da cin hanci da rashawa ganin yadda matsalar ke kassara tattalin arzikin kasar nan.

Kwamishiyar mata ta jihar Kano Malama Zahra’u Umar ce ta yi wannan kiran ya yin wani taron bita da ma’aikatar kula da harkokin mata da hukumar karbar korafe korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar kano suka shirya don tattauna matsalolin dake addabar mata.

Malama Zahra’u ta kara da cewa mata suna da rawar da zasu taka wajen dakile ayyukan cin hanci da rashawa ta bangaren janyo hankalin mazajensu da su guji karbar na goro.

A nasa jawabin shugaban hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar kano Muhuyi Magaji Rimin Gado ya ce mata basu faya karbar cin hanci ba.

Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya ruwaito cewa mata da dama ne suka hallarci taron na wayar da kan mata akan cin hanci da rashawa.

 

Continue Reading

Now Streaming

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!