Connect with us

Siyasa

Tattalin arziki yana kara bunkasa sakamakon rufe kan iyakoki –Hafizu Kawu

Published

on

Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Tarauni Hafizu kawu ya bayyana cewa, tattalin arzikin Najeriya na dab da bunkasa duk da kukan da wasu ke yi bisa rufe kan iyakokin hasar nan.

Hafizu Kawun dai ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Kowane Gauta na nan Freedom Radio.

Ya ce akwai yiwuwar tattalin arzikin ya bunkasa sakamakon daukar matakan da gwamnatin tarayya ta yi a fannoni da dama.

Ya kara da cewa, babban bankin kasa CBN ya fitar da rahoton cewa nan da shekara mai kamawa tattalin arzikin kasa zai habaka bisa yadda aka dakatar da shigo da wasu kayayyaki inda harkokin noma za su kara inganta.

Ya kara da cewa, binciken na CBN ya bayyana cewa duk shekara ‘yan Najeriya na shigo da shinkafa ta kimanin dala biliyan 5, inda yanzu haka noman shinkafa ya fara habaka sakamakon dakatar da shigo da shinkafar.

RUBUTU MASU ALAKA:

Babu banbanci tsakanin jam’iyyun APC da PDP –Bashir Jantile

Muntari Ishaq ya can-can ci zama kwamishina -Aminu Mai dawa

Siyasa: Muntari bai can-canci zama kwamishina ba –Hamza Darma

Continue Reading

Siyasa

Muna rokon gwamna Ganduje ya sulhunta Muntari da Sha’aban –Habib Sadam

Published

on

Daya daga matasan ‘yan siyasa na karamar hukumar birni da kewaye Habib Sadam Makwarari ya roki gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da ya sasanta manyan bangarori biyu na jami’iyyar APC a karamar hukumar.

A cikin shirin Kowane Gauta na nan Freedom Radio Habib Sadam ya bayyana cewa

“Ni dan karamar hukumar birni ne gaba dayan su ba inda babu dan uwana, ko ta auratayya ko ta musulunci ko ta zamantakewa, ba wanda ba dan uwana ba a ajiye maganar siyasa, wannan maganar za ta iya haifar mana da da mara ido”

Ya kara da cewa dukkan bangarorin dake da sabani da juna ‘yan uwana ne kuma ko babu siyasa cikin su za mu koma, a don haka yake rokon gwamnan ya yiwa Allah da ma’aiki ya shiga tsakanin bangarorin domin gudun kada rikicin ya rikide ya koma kan mallam talaka a cewar sa.

Rubutu masu alaka:

Dokar tsaftacce soshiyal midiya ba zata yi tasiri ba – Aminu Mai dawa

Muntari Ishaq ya can-can ci zama kwamishina -Aminu Mai dawa

 

Continue Reading

Siyasa

Dokar tsaftacce soshiyal midiya ba zata yi tasiri ba – Aminu Mai dawa

Published

on

Fitaccen dan siyasar nan Alhaji Aminu Maidawa Fagge ya bayyana cewa ko kadan dokar tsaftace shafukan sada zumunta da gwamnati tayi ko kadan ba ta magance komai ba.

Maidawa ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Kowane Gauta na nan Freedom Radio inda ya bayyana cewa ga hukumomi nan irin su EFCC an kafa su da kyaky-kyawar niyya amma yanzu sun koma aiki ga wani bangare guda daya.

Sannan ya kara da cewa za’a iya yin amfanin da wannan doka wajen hana masu adawa da gwamnati damar bayyana kura-kuran da gwamnati ke tafkawa.

Rubutu masu nasaba:

Shariar Ganduje da Abba: Jamiyyar PDP na zargin sauya Alkalai

Muntari Ishaq ya can-can ci zama kwamishina -Aminu Mai dawa

Continue Reading

Manyan Labarai

Kano:APC ta musanta zargin sauya ra’ayin kotun daukaka kara

Published

on

Jamiyyar APC ta musanta zargin da jamiyyar mai hammaya ta PDP ke yi mata na yunkurin amfani alkalan da zasu saurari karar zaben gwamna daza’a gudanar a Kaduna.

Jaridar KanoFocus ta rawaito cewar idan za’a iya tunawa jam’iyyar PDP ta bayyana wannan zargi na ta ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar lahadi din da ta gabata.

Kwamishinan yada labarai Muhammad Garba ne ya bayyana zargin da jamiyyar PDP ke yi a matsayin , cewar ba gaskiya ba ce wani yunkuri ne na shafa jamiyyar APC kashin kaza domin aga baiken ta a idon al’ummar jihar Kano, tare da shafawa kotun daukaka kara laifin .

Mal Muhammad Garba a cikin sanarwa ya bayyana cewa ko a jiya litini da jamiyyar PDP ke yada wannan sanarwa mai ciki da Kazafi, kuma takan yi haka ne da zarar ta fuskanci cewar ba zata yi nasara ba .

Shariar Ganduje da Abba: Jamiyyar PDP na zargin sauya Alkalai

Ya ce APC da dan takarar ta suna da yakinin sakamakon da za’a samu bayan sauraron karar a kotun daukaka kara za’a gudanar da shi cikin adalci ne .

Ya ce gwamnatin jihar Knao ba zata yarda jamiyyar PDP ta haifar da abinda zai kawo rudani da tada zaune tsaye ba kamar yadda sanarwa ta bayyana.

Continue Reading

Now Streaming

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.