Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Hukuncin kotun koli :Shin Atiku ya hakura da shugabancin Najeriya?

Published

on

A ranar laraba talatin ga watan Oktobar da muke ciki ne kotun koli ta kori karar da dantakarar shugaban kasa a jamiyyar PDP , Alhaji Atiku Abubakar ya shigar gabanta ,yana kalubalantar nasarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a zaben ranar 23 ga watan Fabrairu na shekarar bana.

Bayan kotun sauraran kararrakin zaben shugaban kasa a watan Satumba ta kori karar da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya shigar, sai ya garzaya kotun koli inda itama tayi watsi da karar da ya shigar a gabanta.

Shi dai tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya dade yana neman ya shugabanci Najeriya a tarihin siyasar kasar nan ,tun lokacin da sojoji suka rika kokarin dawo wa da Najeriya turbar dumokradiyya.

A lokacin rusashshiyar jamiyyar SDP Atiku Abubakar ya nemi tsayawa takarar shugaban kasa ,wasu dalilai suka saka Atiku Abubakar bai yi takarar ba ,wanda daga bisani ya tsaya takarar gwamnan sabuwar jahar Adamawa kafin tsohon gwamnan na jahar ta Adamawa marigayi Saleh Michika na rusasshiyar jamiyyar NRC yayi nasara akan Alhaji Atiku Abubakar, inda ya zama gwamnan jahar ta Adamawa.

Da tafiya tayi tafiya wasu daga cikin jiga jigan jam’iyyar SDP sun nemi tsohon dantakarar shugaban Najeriya chief Moshood Kashimawo Olawale Abiola da ya tafi da Atiku abubakar a matsayin mataimakinsa, amma sai gwamnonin jamiyyar SDP suka kekasa kasa suka hana Chief MKO Abiola ya dau Atiku ya dafa masa a matsayin mataimakin shugaban kasa.

Chief Moshood Kashimawo Olawole Abiola ya dauki Alhaji Babagana Kingibe a matsayin abokin takarar sa ,inda ake zatan sun lashe zaben ranar 12 ga watan Yuni da gwamnatin tsohon shugaban kasa janar Ibrahim Badamasi Babangida ta soke da ya jawo rigingimun siyasa a fadin tarayyar Najeriya.

Bayan dawowa mulkin dumkradiyya tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya lashe zaben gwamnan jahar Adamawa a karkashin tutar jam’yyar PDP.

Kafin a rantsar da gwamnonin Najeriyar a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 1999 dantakarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Janar Olusegun Obasanjo ya dauki Atiku Abubakar ya rufa masa baya , jim kadan bayan ya lashe zaben shekarar 1999 da kusan kuri’u miliyan goma sha takwas.

An rantsar da Chief Olusegun Obasanjo shi da Alhaji Atiku Abubakar a filin Eagle Square dake birnin tarayya Abuja ,jim kadan bayan tsohon shugaban kasa Janar Abdulsalami Abubakar ya mikawa Chief Olusegun Obasanjo mulkin Najeriya.

Daga nan ne fitilar Atiku Abubakar ta rika haskakawa a siyasa , inda wasu suka zarge shi da cewa yayi kokarin tumbuke mai gidan sa Chief Olusegun Obasanjo a zaben fitar da gwani na shugaban kasa da ake sa ran  yi a shekarar 2003.

Wannan dalili ne yasa rahotanni suka yi nuni a wancan lokacin cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo sai da ya tsuguna ya roki mataimakin nasa da ya taimake shi ya sake samun karo na biyu wanda shi kuma daga bisani zai rufa masa baya a zaben shekarar 2007 .

Da zaben shekarar 2007 yake karatowa ne Atiku Abubakar ya rika shan mazga irin ta siyasa a hannun maigidan sa Olusegun Obasanjo ,wanda daga baya hakan ba ta saka Atiku Abubakar ya cimma manufar sa ta gadon maigidan sa Cif Olusegun Obasanjo akan karagar mulki ba.

Sai da ta kai Atiku Abubakar ya canja sheka zuwa jamiyyar AC, amma zargin tabka magudi da aka yi a zaben shekarar 2007  ta saka Cif Olusegun Obasanjo yayi nasarar dora marigayi Umaru Musa Yar’adua akan karagar mulkin Najeriya.

A shekarar 2011 Atiku Abubakar ya sake neman jamiyyar PDP ta tsayar da shi takarar shugaban kasa amma bai yi nasara ba, inda Dr Goodluck Ebele Jonathan ya samu tsayawa.

Amma a shekarar 2014 lokacin zaben fitar da gwani na jamiyyar APC Atiku Abubakar shi da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da tsohon gwamnan jahar Imo Rochas Okorocha da tsohon gwamnan jahar Kano Rabiu Musa Kwankwaso sun gwada kwanji amma shugaba Muhammadu Buhari yayi nasara akan su.

Sai gashi a shekarar bana (2019)Atiku Abubakar ya sake tsayawa a jamiyyar PDP bayan ,yayi mata kome amma bai yi nasara ba inda ya garzaya kotu ,su kuma kotunan suka kori karar.

A yunkurin sa na neman shugabancin kasar nan sau hudu, shin Atiku Abubakar ya hakura duk da cewa kuma shekarunsa na karuwa ?.

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!