Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shugaban kasa ya taya wazirin Dutse murnar cika shekaru 70

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Wazirin Dutse Alhaji Bashir Dalhatu murna wanda ya cika shekara saba’in da haihuwa a jijya Alhamis.

Muhammadu Buhari y ace  taya murna ga Bashir Dalhatu ya zama wajibi kasancewar  Allah ya albarkaci rayuwar sa cikin wannan shekaru masu yawa da yayi a duniya,.yana aikin gwamnati da kuma bangarori masu zaman kan su.

Sakon taya murnar na kunshe cikin sanarwar da babban mai taimakawa shugaban kasa kan kafafan yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar a Abuja a jiya Alhamis.

Haka zalika shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya alummar masarautar Dutse da ‘yan uwa da iyalai da abokan Wazirin Dutse Alhaji Bashir Dalhatu wanda ya taba rike mukamin ministan kula da al’amuran cikin gida da kuma ministan wuta da mumula karafa kuma ya taba zama babban sakatare a ma’aikatar sufuri da jiragen sama.

Gwamnatin Jigawa ta rage wa ma’aikata lokacin aiki

Jigawa:Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da mutuwar mutane 7 a wani batsari da ya afku

Fadar shugaban kasa ta aike da ta’aziyar ta ga Iyalan Tafawa Balewa

A cewar sanarwar shekarun Alhaji Bashir Dalhatu da yayi wajen bautawa kasar sa a matsayin sa na kwararren lauya  ba zata taba mancewa da sub a, kuma ba za’a taba Ambato tarihin kasar nan ba tare da sanya irin gudunmawar da ya  bayar ba.

A don haka sanarwar ta kara da cewar shugaban kasa ya bukaci da ya cigaba da hidimtawa kasar nan ba tare da gajiyawa ba.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!