Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Za a fara koyar da harshen China a jami’ar Bayero

Published

on

Jami’ar Bayero da ke Kano, ta ce nan gaba kadan za ta fara koyar da harshen kasar China.

Jami’ar ta sanar da hakan ne a shafinta na Intanet jim kadan bayan sanya hannu kan yarjejeniyar fahimta juna da ofishin jakadancin kasar China.

Da yake sanya hannu kan yarjejeniyar, Babban jami’i mai kula da harkokin al’adu na ofishin jakadancin China Mista LI Xuda, ya ce, jami’ar Bayero ta kafa tarihin da suka ga dacewar yin hadin gwiwa da ita don samar da irin wannan ci gaba.

Li Xuda ya kara da cewa, kafa cibiyar shakka babu za ta taimaka wajen samar da kwararru a harshen China, da hakan ka iya bunkasa alaka dake tsakanin kasashen biyu musamman ma a bangaren kasuwanci.

Da yake jawabi bayan kammala sanya hannun, Shugaban Jami’ar Bayero Farfesa Muhammad Yahuza Bello, wanda ya samu wakilcin mataimakin sa mai kula da harkokin karatu Farfesa Adamu Idris Tanko cewa ya ce,  jami’ar ta jima tana hada gwiwa da wasu jami’oin kasar China wajen bunkasa sha’anin koyo da koyarwa.

Farfesa Adamu Idris Tanko ya kara da cewa, jami’ar za ta fito da sabon tsarin koyar da harshen kasar China ga ‘yan kasuwa, don basu damar bunkasa yanayin kasuwancin su.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!