Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kwamishinan ‘Yan sandan jihar Kano ya ziyarci gidansu matashin da dan sanda ya harbe

Published

on

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano CP. Habu Ahmed Sani ya kai ziyarar ta’aziyya gidansu matashinnan marigayi Mus’ab Sammani da wani dan sanda ya harbe a makon da ya gabata, tawagar kwamishinan ta ziyarci gida dake unguwar Dantamashe a yankin karamar hukumar Ungogo dake nan Kano a safiyar yau.

CP. Habu Ahmed Sani ya bayyana cewa, yana kan hanyar sa ta zuwa birnin tarayya Abuja don hallatar wani muhimmin taro sai ya samu labarin faruwar al’amarin, kuma nan take ya juyo zuwa Kano inda ya bada umarnin fara bincike kan lamarin.

Ya zuwa yanzu tuni aka cafke dan sandan da ake zargi kuma an gurfanar da shi a gaban kotun ‘yan sanda domin girbar abinda ya shuka.

Kwamishinan ya kara da cewa, mutuwar matashin ba rashi bane ga iyayensa kadai har ma ga al’ummar Kano baki daya, adon haka za suyi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da daukar mataki akai.

Hoto a yayin ziyarar

Tun faruwar al’amarin dai mataimakan kwamishinan ‘Yan sanda na jihar Kano sun kai ziyarar ta’aziyya gidan su marigayin.

Yayin ziyarar ta kwamishinan

Shima a nasa bangaren, mahaifin marigayin wato Mus’ab, Alhaji Sammani yayi godiya matuka tare da jinjinawa rundunar ‘yan sanda kan kokarin da take yi na bibiyar wannan al’amari, domin hukunta wanda ake zargi.

Sannan ya kara da cewa mutuwa karar kwana ce ga duk wanda ya kwanansa ya kare.

Labarai masu alaka:

Rundunar ‘yan sanda ta Kano ta yi holin masu yin garkuwa da mutane

Yan film sun karrama kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano

Jihar Kano ta sami sabon kwamishinan ‘yan sanda

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!