Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Magidanci ya kashe dansa a Kano

Published

on

Rundunar Yansanda ta Kano ta samu nasarar cafke wani magidanci bisa kashe dansa dan kimanin shekara uku .

Magidancin mai suna Musbahu  mazaunin unguwar mahaukaci dake karamar hukamar Gaya ya zubawa dan nasa shinkafar bera a cikin abinci  sanadiyyar haka ne yaron ya rasu.

A zantawar da wakilin mu Abba Isa Muhammad yayi da magidancin ya bayyana  cewa ya aikata haka ne soboda yasamu yaran ne bata hanyar aure ba kuma ba shi da mahaifiya da zata rike masa yaron shi yasa ya kasha dan,amma kuma ya nemi da a sassauta masa bisa abun da ya aikata.

Kakakin rundunar yansanda ta Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa yace da zarar sun gama bincike zasu mika mai lefin zuwa Kotu domin ya fuskanci hukunci.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!