Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Shekara daya da rasuwar Shagari: Irin ayyukan da yayi wa Najeriya.

Published

on

Tso

A ranar 28 ga watan Disambar shekarar 2018 a yammacin Juma’a Allah yayiwa tsohon shugaban Najeriya farar hula na farko rasuwa ,Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari.

Tsohon shugaban kasa Shagari ya rasu ne a babban asibitin kasa dake Abuja inda daga bisani gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya karbi gawar sa a filin jirgin sama na Sultan Abubakar III a garin Sokoto.

An haifi Marigayi Alhaji Shehu Shagari a ranar 25 ga watan Fabrairun shekarar 1925 a garin Shagari dake Jihar Sokoto.

Alhaji Shehu Shagari shahararran dan siyasa ne kuma yana daga cikin na gaba gaba wajen kafa jam’iyyar NPC a jamhuriya ta farko .

Tsohon shugaban kasa Shagari yayi minista a gwamnatin    Firaminsita Abubakar Tafawa Balewa inda yayi ministan harkokin tattalin arziki da sauran su.

Lokacin da aka tumbuke gwamnatin Sir Abubakar Tafawa Balewa a ranar 15 ga watan Janairun 1966 Alhaji Shehu Shagari na daya daga cikin wadanda suka yi kokarin ganin an bi tsarin Mulki domin mika gwamnati ga mataimakin Firaminista Zanna Bukar Diprachima.

Amma shugaban majalisar dattijai na wancan lokacin Dr Nwafor Orizu wanda shi ne ya kamata ya gayyaci kafa gwamnati da Zanna Bukar Diprachima zai shugabanta yaki.

Nwafor Orizu ya gayawa Shugaba Shagari da mukarrabansa cewa su koma gida sai an neme su ,wannan dalili ne ya saka ta babban gidan Rediyo na Najeriya suka ji Dr Nwafor Orizu na gayyatar tsohon Shugaban kasa Manjo Janar Thomas Umunakwe Aguiyi Ironsi ya yi wasu jawabi inda daga baya hakan ta saka Ironsi ya kafa gwamnati.

Janar Olusegun Obasanjo na mika mulki ga Shugaba Shagari a ranar 1 ga watan Oktoban 1979.

Bayan da aka rusa gwamnatin su ta farko Shugaba Shagari ya koma jihar sa ta asali wato rusasshiyar Jihar Arewa maso yamma mai shalkwata a Sokoto inda ya zama kwamishinan ilimi a gwamnatin Assistant Commissioner Usman Faruk.

Gwamnatin tarayya ta sake gayyatar Alhaji Shehu Shagari karkashin gwamnatin Janar Yakubu Gowon inda ya zama Ministan harkokin tattalin arziki wanda a lokacin ana kiran minista da Federal commissioner , bayan nan ne akayi masa sauyin ma’aikata ya koma ministan kudi wato Federal commissioner of Finance.

SHIGAR SA SIYASA

Tun jamhuriya ta farko Alhaji Shehu Shagari dan siyasa ne goggage amma lokacin da sojoji suke shirin mika mulkin Najeriya ga hannun farar hula lokacin da aka kafa jam’iyyu a shekarar 1978 Shugaba Shagari ya yi niyyar ya fito takarar danmajalisar dattijai ne wanda daga bisani ya canja shawara.

An yi zaben fitar da gwani na shugaban kasa a jamiyyar NPN inda Alhaji Shehu Shagari yayi takara da Marigayi Malam Adamu Chiroma da Marigayi Danmasanin Kano Yusuf Maitama Sule .

A zaben shugaban kasa da aka yi a watan Agustan shekarar 1979 Shehu Shagari ya lashe zabe da kuri’a fiye da miliyan biyar inda ya doke abokan takarar sa, da suka hada da Marigayi  Chief Obafemi Awolowo na jamiyyar UPN da Dr Nnamdi Azikiwe na jam’yyar NPP da Malam Aminu Kano na jam’iyyar PRP da Alhaji Ibrahim Waziri na jami’yyar GNPP.

RANTSAR DA SHI DA AYYUKAN RAYA KASA.

Bayan da tsohon shugaban kasa Janar Olusegun Obasanjo ya mikawa Alhaji Shehu Shagari Mulki ya fara cika alkawarurrukan da ya dauka a yakin neman zabe ,daga cikin ayyukan da Alhaji Shehu Shagari yayi wa Najeriya sun hada da gina gidaje a kowacce shalkwatar jiha, a lokacin Najeriya na da jihohi 19.

Wadannan gidaje su aka rika kira da Shagari Quarters,bayan wannan Marigayi Shugaban kasa Shagari ya gaggauta fara aikin cigaban sabon birnin tarayya Abuja, inda ya cigaba da yiwa birnin ayyukan samar da gadoji da tituna da gidan shugaban kasa.

Alhaji Shehu Shagari ya kafa kamfanunuwan mulmula karafa na Osogbo steel rolling mill da Ajaokuta Steel company.

Ya samar da gidaje na musamman a birnin Legas.

Shugaba Shagari ya sake lashe zaben shugaban kasa karo na biyu a watan Agustan shekarar 1983, an kuma sake rantsar da shi a ranar 1 ga watan Oktoban Shekarar 1983.

TUMBUKE SHI DAGA MULKI DA SOJOJI SUKA YI.

Watanni uku cif da fara wa’adin sa na Mulki a karo na biyu ,sojoji a shekarar 1983 ranar 3 1 ga watan Disamba suka tumbuke shugaba Shagari daga mulkin Najeriya ,suka kuma nada Manjo Janar Muhammadu Buhari wanda shi ne shugaban kasar Najeriya a yanzu.

RASUWAR SHAGARI

Alhaji Shehu Shagari ya rasu da yammacin juma’a ranar 28 ga watan Disambar shekarar 2018 yana da shekaru 93 da watanni goma a Duniya.

An yi janaizar sa a Jihar Sokoto wanda shugaban babban masallacin Abuja Farfesa Shehu Ahmad Galadanchi ya jagoranta.

Janaizar Shugaba Shagari a Shagarin Sokoto a ranar 29 ga watan Disambar 2018.

Allah ya gafarta masa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!