Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Babagana Zulum: Magajin Sardauna

Published

on

Daga Abdullahi Isa

Tun bayan da kasar nan ta dawo tsarin mulkin Dimukuradiya a alif da dari tara da casa’in da tara (1999), ban yi laifi ba inna ce kasar nan ko Kuma lardin Arewa ba a samu gwamna na wata jiha da al’amarinsa ke bai wa kowa mamaki kamar gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ba.

Wato al’amarin wannan bawan Allah abin mamaki ne wanda kusan kowa a kasar nan ke mamaki da Kuma buga ayoyin tambayoyi daban-daban cewa wai dama a kasar nan akwai ‘yan siyasa da ke da jajircewa da sanin ya kamata da kwazo da Kuma kishin al’ummar sa irin haka.

Tabbas Wannan zance ne da al’ummar kasar nan da dama ke yi game da irin namijin kokari da Kuma sanin makamar aiki irin na gwamna Farfesa Babagana Umara Zulum na jihar Borno. Sanin halin da jihar Borno ke ciki ba wani boyayyen abubane kasancewar ta jiha da ta fi kowace jiha shan dan karen wahala sakamakon rikicin Boko Haram Wanda yayi sanadiyar raba dubban alummar jihar da wasu jihohin Arewa maso gabashin kasar nan da gidajensu, ba ya ga wadanda su ka rasa rayulansu. A lokaci irin wannan babu abinda jihar Borno ke bukata fiye da samun gwamna na gari mai tsoron wanda zai sadaukar da rayuwarsa wajen bautawa al’umma.

Addu’oi da alummar jihar Borno su ka rika yi tsawon Shekaru na fitar da su daga mawuyacin halin da su ke ciki ya amsu watakila hakan ne ya sa Allah ya turo da Babagana Umara Zulum a matsayin gwamna domin share musu hawaye.

Kafin in yi nisa cikin wannan rubutu ta kamata mu dan duba muga ko waye Babagana Umara Zulum.

An haifi Farfesa Babagana Umara Zulum a karamar hukumar Mafa da ke jihar ta Borno a alif da dari tara da sittin da Tara (1969), ya Kuma yi makaranta a garin Mafa da Monguno sannan ya halarci Jamiar Maiduguri da Kwalejin fasaha ta Ramat. Farfesa Babagana Umara Zulum, Inijiya ne a fannin noma ya kuma koyar a Jami’ar Maiduguri, sannan ya taba zama shugaban kwalejin fasaha ta Ramat.

Haka zalika gwamnan jihar na Borno ya taba zama kwamishina a ma’aikatar da ke kula da sake tsugunar da wadanda rikicin Boko Haram ya shafa, wanda mukamin da ya rike kenan na karshe kafin kasancewar sa gwamna a jihar ta Borno a zaben da ya gudana a shekarar da ta gabata.

Watakila wani zai ce bai wa Farfesa Babagana Umara Zulum wannan ma’aikata yana alaka da irin jajircewa da gaskiya irin nasa ya sa gwamnan jihar Borno na lokacin Kashim Shettima ya damka mishi wannan gagarumin aiki, wanda Kuma duk wanda ya bibiyi irin ayyukan alheri da gwamnatin jihar Borno ta gudanar wajen sake tsugunar da mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa musamman wajen gina sababbin gidaje zai fuskanci dalilin da ya sa tsohon gwamnan ya dage wajen ganin Babagana Umara Zulum ya gajeshi.

Wani bangare da wannan bawan Allah ya yi shura shine wajen shiga lunguna da sakuna na jihar da ke fama da rikicin Boko Haram, wato ba wai zuwa kawai da ya ke yi shine abin dubawa ba, gwamnan ya kan ziyarci kauyukan sannan ya je ya zauna da al’ummomin kauyen ya kwana da su cikin kauyen . Kai! Wannan babban lamari ne da ba a taba ganin shi a kasar nan ba, ba dai wannan lokaci ba watakila sai dai a jamhuriya ta farko.

Ba wai kawai nan gwamna Babagana Umara Zulum ya tsaya ba, ya Kuma shahara wajen gudanar da ayyukan raya kasa da za su taba talaka na kasa kai tsaye, ko da ranar daya ga watan nan da muke ciki yayin da wasu gwamnonin su ke gudanar da bukukuwa wajen yin tarurruka da kashe kudaden alumma da sunan bukukuwar sabuwar shekara, shi ko gwamna Babagana Umara Zulum, ya garzaya cikin kauyuka ne wajen kaddamar da ayyukan raya kasa guda biyar wadanda gwamnatin sa ta gudanar wadana suka hada da asibitoci da aikin samar da ruwan sha.

Gamji Magajin Sardauna Farfesa Babagana Umara Zulum ya sake bai wa alummar kasar nan kan kalaman da ya yi game da tambayar sa da aka yi na yawan shiga hatsarin da ya ke wajen kutsawa maboyan Boko-haram, inda ya ce, shi bai zama gwamna don ya yi Wasa ba sai don kawai ya taimakawa alummar sa wajen rage musu radadin mawuyacin halin da su ke ciki.

”Ina tabbatar muku ko da zan rasa raiba akan wannan aiki bana haufi, domin akalla zan samu amsar da zan bayar a lahira”. Allahu Akbar! Ka ji fa. Wannan a Shekarun ba ya in aka ce za a samu gwamna irin haka a kasar nan zai yi matukar wahala jama’a su yadda, ko ni kaina da nake wannan magana zan sa ayar tambaya.

Ko da a jiya litinin shida ga watan Disamba, kallo ya koma jihar Borno batan da gwamna Babagana Umara Zulum ya tuhumi dakarun kasar nan da ke aikin samar da tsaro a jihar da rashin kyautawa wajen karbar na goro a wajen masu ababen hawa. A wani faifan bidiyo da ya yi ta yawo a kafafen sada zumunta da wasu jaridun kasar nan an hango gwamnan na Borno cikin fushi yana kalubalantar sojoji da ke wajen wani shingen binciken ababen hawa a hanyar da ta hada Maiduguri da Damaturu babbban birnin jihar Yobe. Gwamna kai tsaye ya farwa sojojin da fada yana mai cewa, ‘yanzu ku ‘yan Boko-haram suna kashe mutane ku Kuma kunanan kuna tare mutane masu ababen hawa akan hanya kuna karbar cin hancin naira dubu-dubu.

Ba ko shakka wannan namijin kokari da gwamnan ya yi wajen fallasa wannan kazamin dabi’a na wasu jami’an tsaron kasar nan ya kara farin jini ga gwamnan inda har ya kai yanzu tuni wasu su ka fara kiraye-kirayen cewa me zai hana gwamna Babagana Umara Zulum ya gaji shugaba Buhari a shekarar dubu biyu da ashirin da uku.
Koma dai me zai kasance nan gaba Allah ne masani, amma ba ko shakka Arewa a karon farko tsawon Shekaru ta samu Magajin Sardauna Sir Ahmadu Bello. Fatan mu anan sauran gwamnonin Jihohin Arewa dama na kasar nan baki daya za su yi koyi da irin wadannan kyawawan halayya na gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum.

Rubutu daga Abdullahi Isah.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!