Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Gwamnatin Kano zata sake gina hukumar jin dadin alhazai

Published

on

Gwmanatin Kano zata sake gina hukumar jin dadin alhazai ta jiha don yin kafada-da-kafada da na zamani wajen gudanar da ayyukan Hajji da na Umar.

Matakin ya biyo bayan amincewa da dokar ta kafa hukumar gyaran fuska da wajen sake inganta harkokin ta.

Kwamishinan yada labarai na jihar Malam MuhammadGarba ne ya sanar da hakan a taron manema labarai jim kadan bayan kamala taron majalisar zartarwa ta jiha, yana mia cewa matakin ya biyo bayan amincewa da lasisi daga hukumar jin dadin alhazai ta kasa NAHCON.

Hukumar alhazai ta Kano zata dauki mazauna Saudiya ma’aikatan wucin gadi

Hukumar jin dadin alhazai ta yiwa maniyyata hajjin bana na Kaduna 2,200 gwajin daukar bayanai

Kasar Saudiya ta tsayar da 3 ga Maris shekara ta 2019 a matsayin ranar rufe karbar adadin alhazai

Malam Muhammad Garba ya sanarwar da cewar nan bada jimawa majalisar zartarwa  zata aike wa majalisar dokoki ta jiha kunshin gyaran don fara aiki da shi.

Gyaran fuskar da aka yi wa dokar hukumar jin dadin alhazan sun hada da kafa sashin yada ilimin addinin musulunci da wayar da kai da kuma kirkiro da sahshin  shari’a don tabbatar da an gudanar da ayyukan Hajji da Umar yadda ya dace.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!