Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Aliko Dangote ya tabbatar da zai sayi Arsenal

Published

on

Aliko Dangote ya sake jaddada kudirinsa na sayan kulub din wasan kwallon kafa na Arsenal, a shekara ta 2021.

Mai kudin nahiyar Afrikan ya bayyana haka ne a yayin da ake wata hira da shi ta jaridar Bloomberg na kwana-kwanan nan.

A wani shiri na David Rubinstein , ya ce Dangote wanda ake da kiyasin ya mallaki kudi da suka kai kimanin fiye da Dalar Amurka biliyan 14  ya bayyana aniyarsa ta sayan kulub din wasan kwallon kafar.

Ya jima yana da burin mallakar kulub din Arsenal ,amma yakan bayyana cewa abinda ya hana shi sayan kulub din kuwa shine a halin da ake ciki yana da wani aikin da ya sa  a gaba wanda zai lakume akalla Dalar Amurka biliyan 20.

Dangote ya ce a yanzu ya fi maida hanakli wajen tabbatar da ganin ya kammala aikin kamfanin, wanda da zarar ya gama abinda zasu sa a gaba kuwa shine sayan kulub din.

“yanzu ba zan iya sayan Arsenal ba , amma tabbas shine abu na gaba da nake sa ran yi.”

A yanzu haka dai Arsenal na karkashin mallakin Stan Kroenke, wanda yake mallaki wani dan kasar Amurka ne.

Dangote, dai yana cikin masu kudi na Duniya inda yake mataki na 96 kamar yadda kididdigar Bloomberg’s Billionaire’s Index, ta bayyana, ya kuma fara harkar kasuwanci ne yana dan shekara 21, inda a shekara ta 2018 ya zamo dan kasuwar da ya fi kowa shahara a nahiyar Afrika sannan ya bayyana kudirinsa na mallakar kulub din.

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!