Connect with us

Labarai

Kano: INEC ta haramtawa ‘yan bautar kasa aikin zabe  

Published

on

Hukumar zabe mai zamankanta ta kasa INEC ta ce babu wani dan bautar kasa da zata tura karamar Hukumar Bebeji domin gudanar da aikin zaben cike gurbi da za’a gudanar a ranar 25 ga watan da muke ciki saboda dalilai na tsaro.

Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano Farfesa Riskuwa Arabi Shehu ne ya bayyana hakan a wani taron Manema labarai dake  gudana yanzu haka a dakin taro na hukumar zabe dake nan Kano.

Farfesa Riskuwa Arabi shehu ya kara da cewa INEC ta dauki ma’aikata ‘yan bautar kasa na jami’ar Bayero ta Kano kimanin su dubu uku da dari hudu da hamsin da shida ta horas dasu kan yadda zasu gudanarda aikin zaben cike gurbi a kananan hukumomin da za’a sake gudanarda zaben cike gurbi jihar Kano.

Shugaban Hukumar Riskuwa Arabi Shehu ya kuma nanata cewa zasu gudanar da zaben cike gurbi cikin gaskiya da adalci domin ganin an yiwa kowacce jam’iyya adalci.

Farfesa Riskuwa Arabi Shehu ya ce daga yanzu har zuwa kowane lokaci hukumar zabe ta jihar Kano INEC tana saran zuwan kayayyakin aikin zaben daga Babban bankin kasa CBN, kuma za su tabbatar an tura kayayyakin zaben zuwa kananan hukumomin jihar Kano akan lokaci.

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito cewa Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano INEC na cewa zata samar da ingantaccen yanayi mai kyau domin ganin an gudanar da zaben cike gurbi cikin kwanciyar hankali da lumana.

 

 

Labarai

Karancin fitowar masu zabe abun tsoro ne- Abdulrazak Alkali

Published

on

Kungiyar karfafawa mutane gwiwa don shiga harkokin dimokradiyya ta jihar Kano tace dimokuradiyya diyya a Najeriya na fuskantar barazana musamman a hannun kowacce jam’iyya mai mulki wanda hakan ke nuna Demokaradiyya a kasar nan bata samu gindin zama ba.

Shugaban kungiyar karfafawa mutane guiwa da shiga harkokin dimokuradiyya ta jihar Kano Kwamared Abdularak Alkali ne ya bayyana hakan ta cikin shirin muleka Mugano na musamman na gidan Radio Freedom a jiya Lahadi daya mayar da hankali kan zaben cike gurbi da aka gudanar a ranar Asabar data gabata.

Kwamared Abdulrazak Alkali ya kara da cewa matukar mutane suka fara yanke tsammanin samun Adalci a zabukan da ake gudanarwa shakka babu, abun ba zai haifar da da mai ido ba duba da irin kura-kuran da jam’iyyun ke tafkawa a lokacin zabe domin ganin ganin Jam’iyyarsu tayi nasara.

 

Abdulaziz Alkali yace zaben cike gurbi da akayi a ranar Asabar data gabata  abun tsoro ne yadda aka samu karancin fitowar jama’a a wasu gurare sakamakon tsoron abunda kaje yazo na tashin hankali musamman yadda jagororin siyasa ke zuwa guraren zabe domin ganin jam’iyyarsu tayi nasara ta ko wane hali.

 

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito Shugaban kungiyar Kwamared Abdulaziz Alkali na cewa abun takaici ne yadda wasu kasashe suka ki amincewa da tura jami’an su masu sanya ido akan zabuka musamman a wannan zaben cike gurbi da ka gudanar a ranar Asabar data gabata sakamakon rashin ingantacciyar demokradiyyar kasar nan.

Continue Reading

Labarai

Sabbin sarakunan Kano sun kai wa Ganduje ziyarar taya murna

Published

on

Sabbin sarakunan 4 da suka hada da Rano da Karaye da Gaya da Karaye sun kai ziyarar taya gwamnan jihar Kano murnar samun nasara ta tabbatar dashi a matsayin gwannan Kano bayan da Kotun Koli tayi a ayyana shi ne ya samu nasara.

A ya yin ziyarar ta sabbin sarkuna sun kawo ziyarar tare da hakiman su .

Ka zalika gwamna ya tarbe  su a dakin taro na Africa House dake fadar gwamnatin jihar Kano.

Ziyarar sun kawo ta daya-bayan-daya, inda Sarkin Karaye ne ya fara zuwa, sai na Rano ,sai wakilin Sarkin Gaya , Sarkin Yakin Gaya Hakimin Ajingi , Alhaji Wada Aliyu Gaya, sai Sarkin Bichi da ya zo daga karshe wato Aminu Ado Bayero .

Continue Reading

Labarai

 Zulum sarkin aiki – Inji masu iya magana

Published

on

Daga Nasiru Salisu Zango

farfesa Babagana Umara Zulum shine Gwamna da yanzu ya zama zakaran gwajin dafi a cikin gwamnonin Nigeria.
Kokarinsa da jajircewarsa wajen kare hakkin talaka a salon mulki irin na salihan baya, shine ya zame masa Jari wajen samun karuwa, ba a jihar Borno Kadai ba har ma a Nigeria baki daya.

Gidan radiyon freedom muryar jama’a zai cigaba da kawo muku Shiri na Musamman akan ayyukan Professor Babagana Umara Zulum gwamnan jihar Borno.

za’a yi ne a tasoshin mu dake Kano da Kaduna.

Shirin zaizo da karfe 7.30 na dare a tashar freedom Kaduna, karfe 8 zuwa 10-10:30 na daren Lahadin a tashar Freedom dake Kano.

HON. Tanimu Tahir Mbaya mataimakin gwamnan jihar Borno a Fannin Yada labarai shine ya dauki nauyin kawo shirin.

A kasance damu Dan Jin kokarin Murucin Kan Dutse Bai fito ba sai da ya shirya.

Rubutu daga Nasiru Salisu Zango

Continue Reading

Now Streaming

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!