Connect with us

Manyan Labarai

Siyasar Kano: Ina makomar Farfesa Hafizu Abubakar?

Published

on

A kakar zaben shekarar 2019 siyasar jihar Kano ta dauki wani sabon salo da masharhanta da dama suka karkatar da alkalumansu a game da yadda siyasar jihar ta Kano ta rika gudana.

Tun a shekarar 2016 ne a watan Maris rigimar siyasa ta barke tsakanin tsohon gwamnan Kano Rabiu  Musa Kwankwaso da gwamnan Kano mai ci a yanzu Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Wannan sabon salo da siyasar ta jihar Kano ta dauka yasa shugabannin majalisar dokokin jihar Kano karkashin jagorancin tsohon shugaban majal  isar  Kabiru Alhasan Rurum suka bukaci Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da ya  cire jihar hula.

A lokacin mafi rinjaye na ‘’yan majalisar ta jihar Kano sun cire jihar hula banda ‘’yan tsiraru daga ciki.

Amma lokacin da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yake mayar da jawabi ya nemi ‘’yan majalisar ta jihar Kano da su yi  masa afuwa shi da tsohon mataimakin sa Farfesa Hafizu Abubakar na su cigaba da saka jar hular har zuwa wani lokaci.

Hakan akayi ta tafiya, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na saka jar hula shi da mataimakinsa har zuwa karshen shekarar 2018.

Amma kafin akai karshen shekarar 2018 din ce mataimakin gwamnan na jihar Kano Farfesa Hafizu Abubakar, ranar 4 ga watan Agusta ya sanar da cewa yayi murabus daga kan kujerar mataimakin Gwamna.

Dalilin haka ne ya saka kujerar ta zama babu kowa har zuwa lokacin da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya tura sunan Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya maye gurbin Farfesa Hafizu Abubakar.

Jim kadan bayan sanarwar Murabus din da yayi, sai Farfesa Hafizu Abubakar ya bayyana komawar sa jam’iyyar PDP inda ya gayawa manema labarai a cibiyar bincike da harkokin nazarin Dumkradiyya ta Mambayya cewa ya bi jagoransa a siyasa wato Injinya Rabiu Musa Kwankwaso zuwa jam’iyyar PDP.

Farfesa Hafizu Abubakar ya koma gidan siyasa na Kwankwasiyya lokacin da ake shirin fitar da ‘’yantakarar gwamna.

Bayan da aka yi zaben fitar da gwani na jam’iyyar PDP sai Abba Kabiru Yusuf da Kwamared Aminu Abdussalam suka bayyana a matsayin  ‘’yan takarar gwamna da mataimaki.

Hakan ta saka wasu ‘’yan takarar na gwamna da suka hada da shi Farfesa Hafizu Abubakar da Malam Salihu Sagir Takai da Architect Aminu Abubakar Dabo da marigayi Sanata Isah Yahaya Zarewa suka bar jam’iyyar ta PDP.

Farfesa Hafizu Abubakar na gaisawa da Shugaba Buhari a fadar Villa

Barinsu jamiyyar ta PDP wasunsu, irin su Architect Aminu Abubakar Dabo da Sanata Isa Yahaya Zarewa suka koma jam’iyyar APC.

Amma Farfesa Hafizu Abubakar tare da  Malam Salihu Sagir Takai sun koma jam’iyyar PRP mai mukulli.

Jamiyyar PRP ta tsayar da Malam Salihu Sagir Takai a dantakarar ta na Gwamna,sannan daga baya Farfesa Hafizu Abubakar ya sake komawa wata jamiyyar duk a tsakanin murabus dinsa zuwa zaben shekarar bara ta 2019.

Idan ba’a farga ba  Yan siyasa zasu yi amfani da Almajirai a matsayin ‘’Yandaba- Sarki Sunusi II

Sarkin Muslim ya bukaci gwamnatin tarayya samar da hanyoyin dakili matsalolin siyasa da addinai

Daga baya kuma Farfesa Hafizu Abubakar ya sake komawa jami’yyar APC, ,sannan daga bisani ya daina  saka jar hula da aka saba ganin sa da ita.

Tsohon mataimakin gwamnan na Kano bayan komawar sa jamiyyar ta APC ,gwamnan jihar Jigawa Muhammadu Badaru Abubakar ya jagoranci  ce su da shi da Architect Aminu Abubakar Dabo da Marigayi Sanata Isa Yahaya Zarewa inda suka gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kafin da bayan kammala zaben shekarar bara ne dai Farfesa Hafizu Abubakar ya rika bayyana a taruka da dama na jam’iyyar APC wanda ya hada da taro Shugaban kasa Muhammadu Buhari lokacin da yazo yakin neman zabe jihar Kano.

Bayan haka yana bayyana a  abubuwa da dama da suka shafi harkokin gwamnatin jihar Kano da  gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje, sannan ya taba kaiwa magajin sa Dr Nasiru Yusuf Gawuna ziyara ofishinsa.

Shi kansa Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya taba daukar tawagar manyan ‘’yan siyasa kafin zabe sun kai ziyara gidan Farfesa Hafizu Abubakar ,daga ciki har da Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya Sanata Malam Ibrahim Shekarau da shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano Alhaji Abdullahi Abbas.

Duk da hakan jama’a na ta dakon su ga shin a siyasance musamman ma a jami’yyar ta APC dake mulkin jihar Kano da na tarayyar Najeriya me Gwamnati zata yiwa Farfesa Hafizu Abubakar.

A matsayin sa na kwarraran Farfesa akan lafiyar abinci anyi dako a ga kowanne matsayi shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bashi bayan komawa kan karagar mulki amma shiru kake ji.

Majalisar Kano ta amince Ganduje ya ciyo bashin Naira Biliyan Goma Sha Biyar

Gwamna Ganduje ya bukaci hadin kan jam’iyyun adawa

Hatta sanda shugaba Buhari ya kai sunayen ministoci wasu sun yi hasashen su ga ko da sunan Farfesa Hafizu Abubakar, sai kwatsam ga sunan Alhaji Sabo Nanono da Manjo Janar Bashir Salihi Magashi.

Masu sharhin al’amuran yau da kullum na ganin cewa a jihar Kano indai ba mukamin Gwamna Farfesa Hafizu Abubakar zai samu ba, sai dai ka mayar da shi mukamin sa na mataimakin Gwamna wadda a yanzu akwai wanda yake kanta.

Duk mukamin da aka bawa Farfesa Hafizu Abubakar sabanin Gwamna ko mataimakin sa a jihar Kano ci baya ne gare shi a siyasa.

 

Manyan Labarai

Bana neman matar Aure-BABANGIDA

Published

on

Tsohon shugaban mulkin sojin kasar nan janar Ibrahim Badamasi Banagida mai ritaya, ya ce, shi kam baya neman wata matar aure.

A wata zantawa da yayi da jaridar Daily Trust, janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya, ya ce, shi ba ya bukatar yin aure a yanzu, saboda duk wata kulawa da ya kamata ‘ya’ya su yiwa mahaifinsu ‘ya’yan sa, na yi masa.

Ya ce, a yanzu  a matsayin sa na dattijo dan sama da shekaru saba’in, yana ga ba ya bukatar sai ya yi aure.

A baya-bayan nan ne dai, rahotanni su  ka yi ta yawo a kafafen yada labarai da ke cewa, tsohon shugaban mulkin sojin na neman matar aure.

A ranar 7 ga watan Disamban shekarar 2009 ne, mai dakin tsohon shugaban kasar, Hajiya Maryam Ibrahim Badamasi Babangida, ta rasu a wani asbiti da ke birnin Los Angles a jihar California da ke kasar Amurka bayan ta yi fama da cutar daji. Tun daga nan dai har ya zuwa yanzu, tsohon shugaban kasar, bai kara yin aure ba.

Continue Reading

Labaran Kano

Rashin tsarin Siyasa na gari, shi ke cutar da Kano- Dattawan Jihar Kano

Published

on

Kungiyar da ke rajin ganin cigaban  jihar Kano mai suna Kano Concern Citizen Initiative, ta ce rashin tsarin siyasa na gari shi ke dankwafe cigaban jihar Kano.

A cewar kungiyar jihar Kano ta na shan fuskantar matsaloli da dama a wannan lokaci sakamakon rashin kyakkyawar tsarin siyasa na gari wanda zai daura jihar a turba mai kyau.

Wannan dai jawabi ne da shugaban kungiyar Alhaji Bashir Usman Tofa ya yi a zantawar sa da manema labarai, bayan kammala taro kan harkokin tsaro wadda kungiyar ta shirya yau a nan Kano.

Ya ce kungiyar ta damu matuka kan irin mawuyacin hali na koma baya ta kowace bangare Wanda jihar ke fuskanta a yanzu, wanda hakan ya sa suka ga ya zama wajibi su kira taron domin nemo mafita.

A nasa bangaren dattijo Alhaji Isah Bayero ya ce dole ne Idan an tashi irin wannan taro a rika duban matsalolin da ya shafi yankin Arewa baki daya saboda halin da ake ciki a Najeriya duk abinda ya shafi jihar Kano to ya shafi Arewa baki daya saboda haka ya bukaci masu shirya taron da su fadada tunaninsu wajen ganin ci gaban yankin Arewa.

A nasa bangaren shugaban cibiyar harkokin kasuwanci ta jihar Kano Alhaji Dalhatu Abubakar ya ce akwai rashin hakuri da Kuma juriya na ‘yan kasuwar jihar Kano ya na taka rawa wajen samun koma baya a harkar kasuwanci.

A cewar sa a lokuta da dama za su samu dama ta taimaka wa Yan kasuwa amma da an kawo tsarin sai Yan Kasuwa su ki zuwa su shiga cikin tsarin, yana mai cewa burunsu kawai kullum suji ance gwamnati za ta raba kudi ga yan Kasuwa nan ne za ka gansu gaba wajen rige-rigen zuwa.

Taron ya amince cewa har sai al’ummar jihar Kano baki daya sun hada kansu sannan za a samu nasarar dakile matsalolin da ke addabar jihar.

Continue Reading

Labaran Kano

Gwamnatin Kano za ta yi rigakafi ga yara sama da miliyan 3

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta ci gaba da yakar cutar shan inna wato Polio, kasancewar cuta ce da ta ke taba laka tare da haifar da shanyewar wani bangare na jikin kananan yara a cikin kankanin lokaci.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana hakan yau a wani taron manema labarai da ya mayar da hankali a kan gangamin rigakafin cutar ta shan’inna da za a gudanar a kananan hukumomi 44 da ke nan jihar Kano.

Dakta Tsanyawa ya kuma kara da jan hankalin iyaye wajen baiwa jam’ian lafiya dake zagayawa gida-gida hadin kai domin yi wa yaransu allurar rigakafin domin hada hannu wajen yakar cutar.

Ya kuma ce a halin yanzu ma’aikatar ta karbi allurai fiye da miliyyan uku da dubu dari shida daga hukumar bunkasa lafiya ta kasa a matakin farko, inda ake sa ran yi wa yara miliyan uku da dubu dari biyu da arba’in da biyu da arba’in allurar, wadanda suke tsakanin watanni 59, inda kuma tuni aka baiwa ma’aikata dubu talatin horo a kan aikin.

Wakiliyarmu Zahra’u Nasir ta ruwaito cewa kwamishinan ya ce tuni ma’aikatar lafiya ta dauki matakan kariya cikin gaggawa domin hana cutar nan ta Corona Virus shigowa jihar Kano.

Continue Reading

Now Streaming

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!