Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zamu sake nazari kan yadda aka jinginar da Rumbunan adana hatsi-Nanono

Published

on

Gwamnatin tarraya ta amince ta samar da hanyoyin da za’a sake yin nazari kan yadda za’a jinginar da rumbunan adana hatsi ko abinci a kasar nan ga kamfononi masu zaman kan su.

Ministan noma Alhaji Sabo Nanono ya bayyana hakan a ya yin da ya kai ziyarar gani da ido wurin rumbun adana hatsi da ya kai girman tan dubu 25 a karamar hukumar Jahun ta Jigawa.

A cewar Alhaji Sabo Nanono gwamnati zata soke lasisin duk wani kamfani da ya gaza kaiwa ga sharudan da aka gindaya wajen kula yarjejeniyar, yana mai cewar, yaje karamar hukumar ne don ganewa idanun sa yadda ake amfani da rumbunan kamar yadda aka kulla yarjejeniyar.

Nan bada jimawa za’a fara fitar da shinkafa zuwa ketare -Nanono

Za’a dawo da ma’aikatun casar Shinkafa a Kano -Nanono

Babu yunwa a Najeriya: Nanono

Kazalika ministan ya nunar cewar, an tanadi runbunan adana kayayyakin abinci kamar su hatsi da Dawa da masara da wake da maiwa da Aca da dai sauran su a sassan kasar nan da nufin  adana su don wadata kasar nan da abinci.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!