Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Mutum miliyan Ashirin na fama da damuwa a Najeriya

Published

on

Kimanin mutum miliyan ashirin ne ke fama da damuwa a fadin tarayyar Najeriya a shekaru uku da suka wuce.

Masanin halayyar dan Adam Farfesa Sani Lawal Malumfashi ne ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da shirin Barka da Hansti na nan Freedom Radio.

Farfesa Malumfashi yace sakamakon wasu al’amura na rayuwa da suka yi wa ‘’yan Najeriya tsamari shi yasa suke aikata wasu abubuwan da basu kamata ba ciki har da kashe kai ko kisan wani.

Shehin Malamin na jamiar ta Bayero ya kara da cewa kwayar halittar wasu ce ta saka suke aikata wasu daga cikin munanan halaye kamar kisan kai tun sanda aka haife su.

Yace kwayar halittar wasu mutanan tana da zafi wasu kuma tana da sanyi.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano tayi zagaye wuraren da ake aikata laifuka

Gwamnatin Gombe ta koka kan yadda ake aikata laifukan fyade

Fafesa Sani lawan ya kara da cewa ko aure mutum zai yi idan yana da zazzafan hali to kamata yayi ya auri mai sanyin hali idan kuma mace na da zafin hali to kamata yayi ta auri mai sanyin hali.

A nasa bangaren Kyaftin Abdullahi Adamu mai ritaya yace idan har bangaren Shariah zai tsayin daka wajen aiwatar da shari’u yadda suka kamata to shakka babu za’a samu raguwar kisan maza da mata ke yi ko kuma kisan mata da maza ke yi.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!