Connect with us

Labaran Kano

Sabo Nanono ya maida martini kan zargin da ake masa

Published

on

Babban Hadimin Ministan noma na musamman Idris Ibrahim Unguwar Gini ya musanta zargin da ake yiwa Ministan ayyukan noma Sabo Nanono akan bayar da kwangilar taki wanda wasu ke ganin ana bayar da ita ne ga shafaffu da mai.

Ibrahim Unguwar Gini ya bayyana hakan ne a zantawarsa da shirin Kowane Gauta na tashar Freedom.

Ya na mai cewar, Ministan Noma ba shi da ikon bayar da kwangila, shugaban kasa shi ke da ikon baiwa kowane Kamfani kwangila, bashi ba kasancewar wasu da dama na ganin cewar ministan ya sabawa ka’ida wajen bada kwangiyar.

Labaran Kano

Rashin tsarin Siyasa na gari, shi ke cutar da Kano- Dattawan Jihar Kano

Published

on

Kungiyar da ke rajin ganin cigaban  jihar Kano mai suna Kano Concern Citizen Initiative, ta ce rashin tsarin siyasa na gari shi ke dankwafe cigaban jihar Kano.

A cewar kungiyar jihar Kano ta na shan fuskantar matsaloli da dama a wannan lokaci sakamakon rashin kyakkyawar tsarin siyasa na gari wanda zai daura jihar a turba mai kyau.

Wannan dai jawabi ne da shugaban kungiyar Alhaji Bashir Usman Tofa ya yi a zantawar sa da manema labarai, bayan kammala taro kan harkokin tsaro wadda kungiyar ta shirya yau a nan Kano.

Ya ce kungiyar ta damu matuka kan irin mawuyacin hali na koma baya ta kowace bangare Wanda jihar ke fuskanta a yanzu, wanda hakan ya sa suka ga ya zama wajibi su kira taron domin nemo mafita.

A nasa bangaren dattijo Alhaji Isah Bayero ya ce dole ne Idan an tashi irin wannan taro a rika duban matsalolin da ya shafi yankin Arewa baki daya saboda halin da ake ciki a Najeriya duk abinda ya shafi jihar Kano to ya shafi Arewa baki daya saboda haka ya bukaci masu shirya taron da su fadada tunaninsu wajen ganin ci gaban yankin Arewa.

A nasa bangaren shugaban cibiyar harkokin kasuwanci ta jihar Kano Alhaji Dalhatu Abubakar ya ce akwai rashin hakuri da Kuma juriya na ‘yan kasuwar jihar Kano ya na taka rawa wajen samun koma baya a harkar kasuwanci.

A cewar sa a lokuta da dama za su samu dama ta taimaka wa Yan kasuwa amma da an kawo tsarin sai Yan Kasuwa su ki zuwa su shiga cikin tsarin, yana mai cewa burunsu kawai kullum suji ance gwamnati za ta raba kudi ga yan Kasuwa nan ne za ka gansu gaba wajen rige-rigen zuwa.

Taron ya amince cewa har sai al’ummar jihar Kano baki daya sun hada kansu sannan za a samu nasarar dakile matsalolin da ke addabar jihar.

Continue Reading

Labaran Kano

Gwamnatin Kano za ta yi rigakafi ga yara sama da miliyan 3

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta ci gaba da yakar cutar shan inna wato Polio, kasancewar cuta ce da ta ke taba laka tare da haifar da shanyewar wani bangare na jikin kananan yara a cikin kankanin lokaci.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana hakan yau a wani taron manema labarai da ya mayar da hankali a kan gangamin rigakafin cutar ta shan’inna da za a gudanar a kananan hukumomi 44 da ke nan jihar Kano.

Dakta Tsanyawa ya kuma kara da jan hankalin iyaye wajen baiwa jam’ian lafiya dake zagayawa gida-gida hadin kai domin yi wa yaransu allurar rigakafin domin hada hannu wajen yakar cutar.

Ya kuma ce a halin yanzu ma’aikatar ta karbi allurai fiye da miliyyan uku da dubu dari shida daga hukumar bunkasa lafiya ta kasa a matakin farko, inda ake sa ran yi wa yara miliyan uku da dubu dari biyu da arba’in da biyu da arba’in allurar, wadanda suke tsakanin watanni 59, inda kuma tuni aka baiwa ma’aikata dubu talatin horo a kan aikin.

Wakiliyarmu Zahra’u Nasir ta ruwaito cewa kwamishinan ya ce tuni ma’aikatar lafiya ta dauki matakan kariya cikin gaggawa domin hana cutar nan ta Corona Virus shigowa jihar Kano.

Continue Reading

Labaran Kano

Wasu mata biyar sun rasa rayukan su a Kano

Published

on

A jiya Alhamis ne wasu mata su biyar suka rasa rayukansu  yayin  yaro guda kuma ya jikkata lokacin da suke tsaka da debar kasa cikin waani ramin tono a kauyen Dauni cikin karamar hukumar Minjibir.

Shaidun gani da a kauyen sun ce matan na tsaka da tono kasar ne a cikin ramin sai kasa ta rubta musu tare da binne su a ciki.

Mazauna kauyen sun bayyanawa Freedom Rediyo cewa matan kauyen dama sun dade suna tono wannan kasa daga ramin suna kawowa kasuwar Kofar-Wambai a babban birnin jiha suna sayarwa.

Shaidun sun kara da cewa tuni dai aka yi jana ‘iza tare da binne mata biyar din da suka rasu a kauyen.

Kazalika  shi kuma yaron da suka ce dan kimanin shekaru biyar ne da aka zakulo da ransa ya samu raunuka, sai dai ba ‘a bayyana ko an kai shi asibiti ba ko a’a.

Rashin kwararrun masu karbar haihuwa ke janyo mutuwar jarirai- Likita

Ana zargin likita da sanadin mutuwar mara lafiya

An zargi jami’an SARS da  sanadiyyar mutuwar wani matashi

Mazauna kauyen dai ba su fadi takamaiman abinda ake yvi da kasar da matan ke kaiwa kasuwar Kofar-Wamban suna sayarwa ba, sai dai wasu sun ce ana amfani da ita ne wajen hada hodar kwalliyar mata.

Jamiin yada labarai na karamar hukumar Minjibir,  Tasi’u Dadin Duniya da kuma takwaransa na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saidu Mohammed Ibrahim sun tabbatar da afkuwar lamarin amma ba su yi karin bayani ba.

 

Continue Reading

Now Streaming

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!