Connect with us

Kiwon Lafiya

Covid-19: Masana sun ce amfani da “Face Mask” kadai ba shi ne mafita ba

Published

on

Darakta mai lura da cututtuka masu yaduwa na ma’aikatar lafiya ta jihar Kano, Dakta Imam Wada Bello ya ce amfani da takunkumin rufe hanci da baki, ba shi ne mafita wajen rigakafin annobar Coronavirus ba.
Cikin wata tattaunawar sa da Freedom Radio, Dakta Wada Bello ya ce matukar mutum ba yana ta’ammali da masu dauke da cutar ba ne, sannan yana lura da tsaftar hannun sa, ta hanyar wanke hannu, tare da kaucewa shiga cunkoso, to bashi da bukatar sanya wannan Takunkumi.
A cewar Dakta Imam sanya wannan takunkumi ba bisa ka’ida ba na iya haifarwa da mutum cutar Coronavirus.

Karin labarai:

Covid19: Gwamnatin Kano ta samar da lambobin kira kan Coronavirus

Ganduje : za’a rufe kan iyakokin jihar Kano COVID-19

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Kiwon Lafiya

Gwamnatin Kano ta fara feshin maganin cutar Covid-19

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce nan ba da jimawa ba za’a fara feshin maganin kashe kwayoyin cuta a Masallatai da Kasuwannin jihar Kano, inda ta ce dole ce ta sanya aka rufe hanyoyin shigowa jihar Kano ba wai son rai ba, kasancewar hakan na cikin hakan na cikin manyan hanyoyin hana shigowar cutar Covid-19 cikin kasar nan.

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Kwamared Muhammad Garba ne ya bayyana hakan jim kadan bayan shirin barka na nan freedom radiyo wanda mayar da hankali kan yadda gwamnati ta bada dokar rufe hanyoyin shigowa jihar nan da dokar zata fara aiki da misalign 12 na daren yau.

Kwamishinan ya kuma kara da cewar, rufe iyakokin jihar nan ne kadai hanyar da za’a bi wajen hana shigowar cutar Corona kasancewar cudanya da juna na cikin manyan hanyoyin kamuwa da ita.

A nasa bangaran kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dakta Kabiru Ibrahim Tsanyawa ya bayyana cewar gwamnatin tana gudanar da aikin Gyaran cibiyar kula da marasa lafiya ta ‘yar Gaya tare da kara inganta wasu daga cikin asibitici da kuma sanya kayayyakin kula da lafiyar a wani bangare na shirin ko ta kwana don yaki da cutar.

Kabiru Ibrahim Tsanyawa ya kuma bukaci al’umma da su kasance masu kula da tsaftar muhalin su tare da bin dokar da gwamnati ta gindaya, tare da bin shawarwarin likitoci da kuma kaucewa shiga cinkoson jama’a.

Continue Reading

Kiwon Lafiya

Covid-19: Kungiyar likitoci NMA ta raba kayan kare kai

Published

on

Kungiyar Likitoci ta kasa reshen jihar Kano ta ce za ta ci gaba da aiki tukuru wajen ceto rayukan al’umma musamman a wannan lokacin da ake fama da cutar Corona a fadin Duniya.

Shugaban kungiyar Likitoci na kasa reshen jihar Kano Dakta Sanusi Muhammad Bala ne ya bayyana hakan yau yayin da yake mika kayayyakin  kare kai ga membobin kungiyar da ke aiki a fadin asibitocin Jihar Kano.

Dakta Sanusi Muhammad Bala ya kuma yi kira ga ‘yan kasuwa da suka kara kudi akan yadda suke amfani dashi wajen kare rayukan al’umma a Asibitocin kasar nan dasu ji tsoron All- su sauko dasu yadda suke ada dan samun tsira anan duniya da kiyama.

Sanusi Muhammad ya kuma nuna takaicin sa bisa yadda a wannan lokacin kayayyakin kare lafiyar al’umma su kai tsada.

Ya kumaja hankalin ma’aikatan kiwon lafiya da su kasance a shirin kota kwana game da ayyukan su, ya kuma yi kira ga ma’aikatan lafiya a fannoni daban-daban dasu hade kansu wajen kare lafiyar Al’umma.

Kungiyar NMA dai ta raba Sinadarin wanke hannu wato hand Sanitizer guda tamanin da abin toshe hanci guda dubu hamsin ga asibitocin dake fadin jihar Kano dan kare lafiyar al’umma.

Continue Reading

Kiwon Lafiya

Yadda Coronavirus ta samo asali – Dr, Bashir Getso

Published

on

Shugaban Kwalejin koyar da aikin tsafta ta Jihar Kano School of Hygiene Dakta Bashir Bala Getso, ya bayyana cewa cutar Corona ta samo asali ne daga haduwar wasu kwayoyin cututtuka masu raunana garkuwar jikin dan adam.

Dakta Bashir Bala Getso ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan tashar Freedom Radio, da ya tattauna kan yadda cutar ke kara yaduwa a kasar nan.

Ya ce cutar na farawa ne daga alamomin mura da sarkewar numfashi, sannan kuma idan har kwayar cutar ta fita daga jikin dan adam ta kan shafe tsawon mintuna talatin kafin ta mutu.

Dakta Bashir Bala Getso ya kara da cewa, cutar ba ta numfashi ake daukarta ba, tana kama dan adam ne ta hanyar taba wasu sassan jiki da hannun da ke dauke kwayoyin cutar.

Ya kuma daukar matakan kare yaduwar ne kadai zai taimaka wajen dakile ta, kamar yadda aka gani a kasar China.

Continue Reading

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 316,348 other subscribers.

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!