Author: Aisha Shehu Kabara

Gwamnatin Jihar Gwambe tayi kan matakin Gwamnatin tarayya

Gwamnatin jihar Gombe ta bayyana rashin jin dadin ta kan matakin gwamnatin tarayya na dakatar da shirin samar da wuraren kiwo da kuma tsugunar da makiyaya a wasu jihohin kasar nan. Gwamnan jihar Alhaji Inuwa Yahaya ne bayyana hakan lokacin da yake ganawar da manema labarai, jim kadan bayan wata ganawar sirri da shugaban kasa […]

JAMB yayi zargi kan zanga zangar adawa da ayyukan hukumar

Shugaban hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta kasa JAMB Farfesa Is-haq Oloyede yayi zargin daukar nauyin zanga-zangar adawa da ayyukan da hukumar ke aiwatarwa. Is-haq Oloyede ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi ga manema labarai yau a birnin tarayya Abuja, tare da bayyana sunan wani dalibi da hukumar ta kwce sakamakon jarrabawar […]

Gwamnatin tarayya ta bayyana kudaden da ake kashewa wajan shigo da madara

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa adadin kudaden da ake kashewa duk shekarar wajen shigo da madara da dangogin ta daga ketare ya tasamma Dala Biliyan daya da miliyan dubu dari uku. Babban sakatare a ma’aikatar noma da raya karkara ta tarayya Dakta Mohammed Umar ne ya bayyana hakan, lokacin da yake jawabi yayin babban taron […]

Tsofaffin Shugabanin Kwamin riko sunyi karar Gwamnan Bauchi

Tsofaffin Shugabannin kwamitin riko na kananan hukumomin jihar Bauchi guda Ashirin sun gurfanar da gwamnan jihar Sanata Bala Muhammed gaban kotu bisa zargin sa da sallamar su batare da wa’adin su ya cika ba. Tsohon shugaban kwamitin riko na karamar Hukumar Bauchi Alhaji Chindo Abdu ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai a […]

Ofishin Akanta na Najeriya ya kalu balancida maganar wasu jaridu

Ofishin akanta Janar na Najeriya ya musanta rahotannin da wasu jaridun kasar  suka yada cewa Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na biyu, ya ce, tattalin arzikin Najeriya  na daf da shiga halin tagayyara. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai Magana da yawun ofishin akanta Janar na kasa, Henshaw […]

Gwanatin Najeriya ta kafa kwamitin da zai kula da hannayen jari

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da kwamitin gudanarwar Hukumar kula da kasuwar hannayen jari ta kasa a jiya Litinin. Babban sakatare a ma’aikatar kudi Alhaji Mahmud Isa Dutse ne ya kaddamar da kwamitin gudnarwar mai kunshe da mutum tara yana kuma karkashin jagorancin Mr Olufemi Lijadu. Kaddamar da kwamitin gudanarwar na zuwa ne shekaru hudu bayan […]

Hukumar hajji ta Najeriya ta rage kudin aikin hajji na bana

Hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON ta rage naira dubu 51, 170 a cikin kudaden da ta ayyana tun da fari a matsayin kudin aikin hajji bana. Wannan na kushe ne cikin wata sanarwa da jami’ar hulda da jama’a ta hukuma00r Fatima Sanda Usara ta fitar da yammacin jiya aka rabawa manema labarai a birnin […]

Ankashe mutane Talatin da biyar a Zamfara

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne, sun kashe mutane talatin da biyar a jihar Zamfara. Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kai harin ne a wasu kauyuka uku da ke yankin karamar Hukumar Shinkafi. Wasu mazauna kauyukan sun shaidawa manema labarai cewa, ‘yan bindigar sun iso garuruwan nasu ne akan akan Babura idan suka […]

An soki Jami’an tsaro da Hukumar zabe kan zaben Jihar kano EU

Kungiyar tarayyar Turai EU ta soki jami’an tsaro da Hukumar zabe ta Najeriya INEC game da rawar da suka taka yayin zaben gwamnan karo na biyu da aka gudanar a nan jihar Kano. A yayin gabatar da rahoto kan zabuka Najeriya da suka gudana a farkon wannan shekara, kungiyar ta EU ta ce, kodayake Najeriya […]

EU tace bata da masaniya kan cewa INEC nada rumbun adana bayanai

Wakilan Kungiyar tarayyar Turai da su ka sanya idanu kan yadda zaben Najeriya ya gudana sun ce basu da wata masaniya game da mallakar rumbun adana bayanai na Hukumar zabe ta Najiya INEC. Rahoton kungiyar ta EU ya yi kafar Ungulu da ikirarin da jam’iyyar PDP da dan takarar ta Atiku Abubakar su ka yi […]