Author: Aisha Shehu Kabara

Abdul’aziz Garba Gafasa ya sake zama shugaban majalisar dokokin jihar Kano

Sabon shugaban majalisar dokokin jihar Kano Abdul’aziz Garba Gafasa, ya sha alwashin tafiya tare da kowa da kowa ba tare da nuna fifikon jam’iyya ba. Abdul’aziz Garba Gafasa, ya bayyana hakan ne yayin zantawa da manema labarai bayan kama rantsuwar kama aiki. Abdul’aziz Garba Gafasa wanda kuma dan majalisa ne mai wakiltar karamar Hukumar Ajingi, […]

Jami’ar Bayero ta yi bikin yaye dalibai karo na 35

Jami’ar Bayero ta Kano ta bayyana aniyarta ta kara kaimi wajen samar da ingantaccen yanayin koyo da koyarwa ga dalibai. Shugaban jami’ar Farfesa Muhammad Yahuza Bello ne ya bayyana hakan yayin bikin yaye dalibai karo na 35 da aka gudanar a dakin taron yaye dailbai dake harabar jami’ar a yau Litinin. Ya ce daya daga […]

Gwamnatin Najeriya zata dauki masu kwarewa a fannin koyarwa

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta dauki dukkannin wadanda suke da kwarewa a bangaren koyarwa musamman wadanda suka samu takardar shaidar malanta kamar yadda ma’aikatar ilimi ta bukata. Babban sakatare a ma’aikatar ilimi ta Najeriya Sonny Echono ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke duba yadda jarabawar neman kwarewa a bangaren koyarwa da cibiyar […]

APC zata yi bincike kan zargin da akewa shugaban ta na kasa

Kwamitin gudanarwar jam’iyyar APC na kasa ya kafa kwamitin ladaftarwa mai kunshe da mutum biyar wanda zai bincike zarge-zargen da mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa mai kula da jihohin arewa Sanata Lawan Shu’aibu, ya yi ga shugaban jam’iyyar na kasa Adams Oshimhole. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren […]

Sarkin Rano ya dakatar da wasu Hakimai

Mai Martaba Sarkin Rano Alhaji Tafida Ila Autan Bawo ya dakatar da Hakimin Tudun Wada Dr Bashir Muhammad da na Karamar hukumar Bebeji Alhaji Haruna Sunusi bisa bijirewa yi masa mubayi’a da suka yi. Wannan na kunshe cikin wata wasika ta musamman da aka aikewa hakiman da ke dauke da sa hannun sakataren masarautar Ranon […]

Sarkin Kano yace zai cigaba da kare mutuncin masarauta

Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu  ya ce za suyi duk mai yiwuwa wajen kare kima da mutuncin masarautar Kano da ma al’ummar jihar Kano baki daya. Muhammadu Sanusi na ya bayyana hakan ne yayin gudanar da addu’ar cika shekara 5 da rasuwar marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero da kuma murnar ciki […]

Mambobin Jam’iyar PDP a majalisar wakilai sun musanta rade-rade da akeyi

Mambobin jam’iyyar PDP a majalisar wakilai sun yi watsi da rade-radin da ke cewa uwar jam’iyyar ta umarce su da su kadawa wani dantakarar shugabancin majalisar ta wakilai kuri’ar su. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai Leo Ogor. Sanarwar ta ruwaito cewa babu […]

An dakatar da hawan Sarki Majalisar masarautar Kano

Majalisar masarautar Kano ta sanar da dakatar da Hawan Nassarawa da Hawan Dorayi da aka shirya za a gudanar a yau Alhamis da kuma gobe Juma’a. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren majalisar masarautar ta Kano Alhaji Abba Yusuf. Sanarwar ta ce dakatar da Hawan na Nassarawa ya […]

An kori jami’an rigkafin Shan Inna su 12 a Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta kori wasu jami’an bada allurar rigakafin shan-inna su 12 sakamakon samun su da laifin karya dokokin bayar da allurar allurar da suka yiwa wasu ‘yara yayinda ake gudanar da shirin. Jami’in lura da asibitin sha ka tafi da ke yankin karamar hukumar Tarauni a nan Kano, Malam Nura Haruna ne ya […]