Author: Umar Idris Shuaibu

KASSOSA: zamu hada hannu da gwamnati wajen yin garambawul a bangaren ilmin kimiyya.

Shugaban kungiyar tsoffin daliban kwalejin Kimiyya ta Dawakin Tofa aji na 1990 Inijiniya Abubakar Ibrahim Khalil ya ja hankalin gwamnatin jihar Kano wajen magance matsalolin da suka dabai-baye sha’anin karatun kimiyya. Injiniya Abubakar Ibrahim Khalil ya bayyana hakan ne yayin taron Sallah karama da kungiyar ta gabatar a dakin taro dake asibitin Aminu koyarwa na […]

An Ja Hankalin Al’ummar Musulmi Kan Kiyaye Iyakokin Allah

  Na’ibin limamin masallacin Juma’a na Sahaba Dakta Abdullahi Muhammad Getso ya ja hankalin al’ummar musulmi kan kiyaye iyakokin Allah a cikin rayuwar su. Dakta Abdullahi Muhammad Getso ya bayyana hakan ne ta cikin hudubar Idin Sallah karama da ya gabatar a masallacin  na Sahaba dake unguwar Kundila a  birnin Kano. Ya ce ya zama […]

kwalejin fasaha ta kano: za mu kara kaimi wajen bunkasa harkokin ilimi

Kwalejin fasaha ta Kano ta bayyana aniyarta ta kara kaimi wajen bunkasa sha’anin koyo da koyarwa  ga dalibai. Shugaban kwalejin Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a kwalejin. Ya ce matakan da suka dauka sun hadar da tantance kwasa-kwasai da ake koyar dasu domin a yarda da su […]

kassosa ta jaddada kudurin ta na ci gaba da bunkasa kwalejojin kimiyya

Uwar kungiyar tsofaffin daliban kwalejojin kimiyya na Kano, KASSOSA ta jaddada kudurin ta, na ci gaba da bunkasa kwalejojin kimiyya dake nan Kano. Shugaban kungiyar, Alhaji Mustapha Nuhu Wali ne ya bayyana haka a wajen taron bude baki da kungiyar ta shirya wa mambobin ta da saukar karatun kur’ani a kwalejin kimiyya ta Mairo Tijjani […]

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano tayi zagaye wuraren da ake aikata laifuka

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano tayi zagaye wuraren da ake gudanar da ayyukan bata gari da rashin tsaro suka kamari. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Muhammad Wakili ne ya bayyana hakan yayin zagayen duba maboyar bata gari a yankunan Badawa da Giginyu dake karamar hukumar Nassarawa. Ya ce rundunar ‘yan sandan jihar Kano tuni ta […]

Kungiyar ICRC ta horas da Fulani dabarun kula da dabbobi

Sarkin Rano Alhaji Tafida Abubakar ya ce, akwai bukatar masu rike da sarautun gargajiya su hada hannu da shugabannin makiyaya domin dakile rikici tsakanin makiyaya da manoma. Alhaji Tafida Abubakar ya bayyana hakan ne yayin bikin yaye makiyaya 30 da suka samu horo kan dabaru da hanyoyin bada agaji ga lafiyar dabbobi wanda kungiyar agaji […]