Author: Baraka Bashir

Majalisar wakilai ta yi barazanar kama shugaban jami’ar Modibbo Adama

Majalisar wakilai ta yi barazanar bayar da umarnin a kama shugaban jami’ar Modibbo Adama da ke Yola, jihar Adamawa, Farfesa Kyari Muhammad saboda gaza bayyana yadda ya kashe kudaden da aka warewa jami’ar a shekarar 2016. Shugaban kwamitin ilimi na majalisar mai kula da manyan makarantu, Alhaji Aminu Suleiman wanda ya mayar da kunshin kasafin […]

Dino Melaye Ya kammala Karatunsa Inji Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello

    Shugaban jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria Farfesa Ibrahim Garba ya shedawa kwamitin da’a na majalisar Dattawa cewa sanata Dino Melaye ya kammala jami’ar a shekara ta 2000.   Shugaban jami’ar ta ABU ya sanar da hakan ne yau yayin da ya bayyana a gaban kwamatin, amma ya ce har yanzu Dino Melaye bai […]

An Gano Jabun Masu Yi Wa Kasa Hidima

    Hukumar kula da ‘yan hidimar kasa ta fada Litinin din nan cewa ta gano jabun ‘yan hidimar kasa da dama bayan da ta bullo da tsarin yin rajista ta hanyar amfani da fusahar intanet ‘yan shekarun da suka gabata. Darakta Janar na hukumar Birgediya Janaral Sulaiman Kazaure wanda ya bayyana hakan lokacin da […]

Sarkin Kano:Malamai Su Samo Sabuwar Manhajar Karatu

  Mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu ya yi kira ga malaman jami’a da kuma Dalibai da su samo wasu hanyoyi na sauya manjar darussa ta hanyar da dalibai zasu rika koyon kimiyya da fasaha da harsunan su na asali.   Muhammad Sanusi ya bayyana hakan ne jim kadan bayan bude sabon masallacin […]

Tsaikon da aka samu na tallafin kasuwar sabon-gari sakaci Ne na Gwamnati

An bayyana tsaikon da aka samu wurin samun tallafin gobarar kasuwar Sabon-Gari a  matsayin wani sakacin daga babban kwamitin nemawa wadanda abin ya shawa taimako. Shugaban hadaddiyar kungiyar ‘yan kasuwar kuma shugaban kwamitin gobarar kasuwar, Alhaji Alin Bagadaza ne ya bayyana haka yau jim kadan bayan kammala shirin ‘Barka Da Hantsi’ na nan gidan rediyon […]

Sarkin Kano Yayi Karin Haske Kan Dokar Matsalolin Aure

Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II ya nemi malamai da sauran Masanan addinin Musulunci su ci gaba da bada gudunmawa don ganin an samar da dokar da za ta rika warware matsalolin aure a tsakanin al’umma.   Malam Muhammadu Sunusi na II na wannan kiran ne yayin wani taron karawa juna sani kan […]

  A ranar 27 ga watan Maris shekara ta 2004 ne al’ummar jihar kano suka bayyana daina amincewa da karbar allurar digon riga-kafi

A ranar 25 ga watan Maris 2003  aka fara kada kuri’u na  kwanakin uku a kasar Rwanda wanda shine karo na farko da aka gudanar da zaben nay an majalisar dokoki a kasar na jam’iyyu da dama , tun bayan samun yancin kai daga kasar Belguim

An Gano Fasahar Kashe Kwarin Dake Harba Kwayar Cutar Tumatur

  Gwamnatin tarayya ta kirkiro da fasahar kashe kwarin dake harba kwayar cutar tumatur ta tota absolute ko kuma ebolar tumatur da Hausa. Wannan cuta dai dake zaman sabuwa a wannan lardi ta sabbaba hasarar miliyoyin naira ga manoman tumatir a bara, musamman a jihohin Katsina da Kaduna da kuma Gombe. Kamar wadannan jihohi, a […]