Author archives: Auwal Hassan Fagge

Akwai bukatar mayar da hankali kan sintirin jami’an tsaro a manyan titina-Abdurrahman Dikko

Daya daga cikin Dattijan Naheriya Malam Abdurrahman Umar Dikko ya ce, amfani da manyan bindigu da ‘yan ta’adda ke yi wajen aikata ta’asa a kan manyan titunan jihohin Arewacin Najeriya abu ne mai matukar tada hankali tare da yin sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama. Malam Abdurrahman Umar Dikko, ya bayyana hakan ta cikin shirin…

Read more

Hukumar jin dadin alhazai ta yiwa maniyyata hajjin bana na Kaduna 2,200 gwajin daukar bayanai

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kaduna ta yiwa maniyyata aikin hajjin bana 2,200 gwajin daukar bayanai ta hanyar dangwalen yatsa domin gudanar da aikin hajjin na bana. Jami’in hulda da jama’a na hukumar Yunusa Abdullahi ne ya sanar da hakan ga manema labarai lokacin da yake bayar da bayanan halin da hukumar ke ciki jiya…

Read more

APC ta bukaci shugaban INEC ya yi sauyin wajen aiki ga shugaban hukumar na jihar Rivers

Jam’iyyar APC ta bukaci shugaban hukumar zabe ta kasa INEC da ya gaggauta sauya wajen aiki ga shugaban hukumar reshen jihar Rivers, Mr. Obo Effanga. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran jam’iyyar, Lanre Issa-Onilu. Sanarwar ta ce sauya wajen aiki ga kwamishinan zaben na jihar Rivers…

Read more

kungiyar ta NLC ta bukaci hukumar INEC ta tabbatar da an gudanar da sahihin zabe a jihohi 6 da ba’a kammala ba

Kungiyar ma’aikatan kwadago ta kasa NLC ta bukaci hukumar zabe ta kasa INEC  da ta tabbatar da an gudanar da sahihin zabe a jihohi shida da ba’a kammala zaben su ba a sassan kasar nan. Haka kuma kungiyar ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sake duba rahoton da kwamitin mai shari’a Muhmmadu Uwais…

Read more

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO