Author: Auwal Hassan Fagge

Marigayi Sani Abacha ya cika shekaru 21 da rasuwa

A yau Asabar 8 ga Yunin 2019 ne marigayi tsohon shugaban Najeriya na mulkin Soja marigayi Janar Sani Abacha ya cika shekaru 21 da rasuwa. An dai haifi marigayi Janar Sani Abacha a jihar Kano a shekarar 1943, wanda ya rasu a rana irin ta yau a shekarar 1998. Marigayin dai ya rasu ne yana […]

Majalisar dattawa ta amince a biya wasu kamfanoni kudaden tallafin mai

Majalisar dattawa ta amince da a biya wasu kamfanoni 67 kudaden tallafin mai da ya kai naira biliyan 129. Hakan ya biyo bayan amincewa da rahoton kwamitin kula da albarkatun man fetur wanda Sanata Kabiru Marafa ke jagoranta. Wannan dai shi ya kawo jimillar naira biliyan 545 da miliyan 900 wanda majalisar dattawa ta amince […]

Hukumar EFCC ta musanta rahoton kama Rochas

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta  EFCC ta musanta rahotannin da ke cewa, ta kama tsohon gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha. A cewar Hukumar ta EFCC babu kamshin gaskiya cikin labaran da ke yawo cewa ta kama Rochas Okorocha. Tun farko dai kafofin yada labarai, sun yi ta yada cewa, hukumar EFCC ta […]

Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane 2 a fadowar ginin Anambra

Rundunar yan sandan jihar Anambra ta tabbatar da mutuwar mutane biyu sakamakon fadowar wani gini a yammacin jiya laraba a garin Onitsha. Mai magana da yawun rundunar, Haruna Muhammad ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a AwKa babban birnin jihar. A cewar sanarwa, ginin da ke lamba 9 a […]

Shugaba Buhari ya yi sammacin gwamnan Katsina

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi sammacin gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, sakamakon ci gaba da kashe-kashen ‘yan bindiga da ke gudana a jihar. Da ya ke tattaunawa da manema labarai a fadar shugaban kasa a daren jiya Laraba bayan tattaunawa da shugaban kasa, gwamna Aminu Masari, ya ce, matsalar ‘yan bindiga a jihar, […]