Author: Auwal Hassan Fagge

JAMB ta saki sakamakon jarabawar UTME na bana

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire ta kasa JAMB ta saki sakamakon jarabawar UTME da dalibai suka rubuta a watan jiya na Afrilu. Shugaban hukumar ta JAMB farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai yau Asabar a Abuja. Farfesa Ishaq Oloyede ya kuma nemi afuwan al’ummar kasar […]

Shugaba Buhari ya bukaci manyan hafsoshin tsaro su kara jajircewa akan aikin su

Shugaban kasa muhammadu Buhari ya bukaci manyan hafsoshin tsaron Najeriya da su kara jajircewa wajen tabbatar da cikakken tsaron rayuka da dokiyoyin al’umma. Muhammadu Buhari na wadannan kalaman ne lokacin da yake ganawa da manyan hafsojin tsaron  a fadar Asorok da ke birnin tarayya Abuja. Shugaban kasar ya kuma bukaci sufeto janar na ‘yan sandan […]

Hukumar NRFF ta nada Yaro a matsayin sabon mai horaswa

Hukumar wasan kwallon Rugby ta Najeriya NRFF ta nada Abubakar Yakubu wanda aka fi sani da Yaro a matsayin sabon mai horas da kungiyar. A cewar shugaban hukumar kwallon Rugby na kasa Kelechukwu Mbagwu an nada Abubakar Yakubu ne da nufin bunkasa kungiyar. Kelechukwu Mbagwu ya ce kwarewar da tshohon dan wasan Rugby Abubakar Yakubu […]

An yi zangazangar kin amincewa da kara masarautu a Kano

Mambobin wata kungiya mai rajin kishin al’ummar Kano da wasu daga cikin mutanen jihar Kano sun gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna adawa da sanya hannun da gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yi kan dokar kara kirkirar Masarautu 4 a jihar Kano. Shugaban kungiyar mai suna Kano First Forum, da mutanen da suka […]

Gwamnatin Jigawa ta rage wa ma’aikata lokacin aiki

Gwamnatin jihar Jigawa ta rage wa ma’aikatan jihar lokacin aiki na awanni 2 a yayin watan azumin Ramadana mai girma na wannan shekara ta 2019. Mai Magana da yawun ofishin shugaban ma’aikata na  jihar ta Jigawa Alhaji Isma’il Ibrahim  ya bayyana hakan a birnin Dutse a jiya Talata 7 ga watan Mayu ta cikin wata […]

Shugaba Buhari ba zan baiwa ‘yan Najeriya kunya ba

Shugaban kasa Muhamamdu Buhari ya ce yana sane da nauyin da ke wuyan sa yana mai yin alkawarin cewa ba zai baiwa ‘yan Najeriya kunya ba, wajen ganin ya tabbatar da kowanne dan kasar nan  ya sami kyakyawar rayuwa. Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne a masalacin fadar gwamnati dake Abuja  yayin da ake gabatar […]

Kawu Sumaila: kafafun yada labarai abokan tafiyar mulkin dumukaradiyya ne

Tsohon mai taimakawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan al’amuran majalisar wakilai ta kasa Kawu Sumaila ya bayyana kafafun yada labarai a matsayin abokan tafiyar da mulkin dumukaradiyya ako ina a Duniya. Kawu Sumaila ya bayyana hakan ne yayin gudanar da rantsuwar sabbin shuwagabannin kungiyar wakilan kafafen yada labarai reshan jihar Kano wanda aka gudanar a […]