Category: Labaran Wasanni

Majalisar dokikin sun ce zasu maida hankali bangaren wassanin

Majalisu dokokin tarayya sun ce za su tabbatar da cewa bangaren wasannin kasar nan sun samu isassun kudade a kunshin kasafin kudin badi.   Mataimakin shugaban kwamitin kula da wasannin ta majalisar Dattawa sanata Kabiru Garba Marafa ne ya bayyana hakan yayin wani taro da aka gudanar a filin wasa na kasa da ke Abuja.

Kano Lions ta samu nasara akan kungiyar Esteem

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Lions ta samu nasara akan kungiyar Esteem boys da ci 3 – 2 a ci gaba da gasar Tofa Premier League da ke gudana mako na bakwai a jihar Kano. Ita ma kungiyar Ashafa action ta casa Gwammaja FC city da ci 2 – 0

ba za’a duko dan wasan da zai maye gurbin Ighalo ba

Jami’in yada labaran kungiyar kwallon kafa ta Super Eagle Toyin Ibitoye, ya ce mai horaswa Gernot Rohr ba zai duko wani dan wasan da zai maye zurbin dan wasan gaban kungiyar Changchun Yatai Odion Ighalo saboda akwai yan wasan da zasu iya maye gurbin sansanin kungiyar a yanzu. Ibitoye ya yi wannan jawabin ne yayin […]

Anthony Joshua, ya yi nasara akan Carlos Takam

Zakaran damben duniya ajin masu nauyi Anthony Oluwafemi Joshua, ya kare kambun sa na ajin masu nauyi na WBA da IBF bayan da ya doke Bafaranshe dan asalin kasar Kamaru Carlos Takam. Joshua mai shekaru 28 wanda iyayen sa ‘yan asalin kasar nan ne ya casa Takam ne a zagaye na goma. Anthony Oluwafemi Joshua […]

Ana zargin kwamitin gudanarwar Kano pillars da mundahana

Kungiyar magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta zargi kwamitin gudanarwar kungiyar ta Kano Pillars da cinye mata mota da tsohuwar gwamnatin Kano ta bata. Shugaban kungiyar magoya bayan Kano Pillars…. ya bayyana hakan a jiya yayin ganawarsa da shugaban majalisr dokokin Kano Yusuf Abdullahi Ata. Shugaban kungiyar ta sai masu gida supporters […]