Gwamnatin Najeriya zata sayi kayan yaki da ta’addanci na Dala biliyan daya

Majalisar kula da tattalin arzikin Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya ta yi amfani da Dala biliyan daya daga cikin Dala biliyan biyu da miliyan dari uku na asusun rarar man fetur domin yakar ta’addanci a arewa maso gabashin Najeriya.

Gwamnonin sun dauki wannan mataki ne yayin taron majalisar karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajoa a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ne ya shaida hakan ga manema labarai na fadar shugaban kasa, bayan fitowar su daga taron a Alhamis din nan.

Godwin Obaseki ya kuma kara da cewa mambobin majalisar suna son a yi amfani da kudin ne domin sayen kayan aikin tsaro da sauran ayyukan hukumomin tsaro, domin murkushe ayyukan ta’addanci.

Share
Share